Fatahu Muhammad, ɗan majalisa da ke wakiltar gunduman shugaban Kasa a majalisar tarayya ya ragargaji masu korafin kada a yi wa soshiyal midiya garambawul kamar yadda gwamnati ta himmatu a kai.
Fatahu wanda yayi jawabi a gaban kwamitin majalisar tarayya dake binciken dakatar da Tiwita da gwamnatin tarayya tayi.
” Me nene Soshiyal Midiya, tsakani da Allah idan ba hauragiya da ruɗani ba. Ina goyon bayan matakin da gwamnati ta ɗauka na yi wa Soshiyal Midiya garambawul domin hakan shine ya fi dacewa idan ana son zaman lafiya a kasar nan.
” Na yi aiki na tsawon shekara 10 a hukumar NCC, kuma na san faɗi tashi da gwagwarmayar da ke yi wajen yakice wasu kalamai da ake yaɗawa a yanar gizo, wanda wasu za su iya tada zaune tsaye da ruɗani a kasar nan.
Fatahu ya ƙara da cewa dole a yi wa Soshiyal midiya garambawul ga idan ana so a samu yi wa matasa iyaka da kawo ruɗani a kasar nan.