MATSALAR TSARO: Buhari ya aika wa Majalisa neman amincewa ya kashe wa tsaro naira biliyan 770.60

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisa da wasiƙar neman su amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira biliyan 895, wadanda a cikin kuɗaɗen, har da naira biliyan 770.60 da ya ce zai kashe ya magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.

Wannan wasiƙa wadda Buhari ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya karanta ta a Zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata.

Ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗin an ce dai zai ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaro wajen ƙarfafa ɓangarorin sojoji da sauran jami’an tsaro.

“Za a kashe naira biliyan 83.56 wajen allurar rigakafin korona. A ciki za a sayi rigakafi samfurin Johnson and Johnson ta naira biliyan 30. Amma a cikin kuɗaɗen akwai ladar hidima, aikace-aikacen da su ka jiɓinci harkokin ayyukan rigakafin korona ɗin.

“Kuma akwai naira biliyan 1.69 na daƙile ƙanjamau. Kuma akwai wasu naira biliyan 40 da za a kashe fannin lafiya, ciki har da kuɗaɗen alawus da albashi da ariyas na ma’aikatan lafiya da fannin ilimi.” Inji Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Usman.

Sannan kuma ta ce akwai naira biliyan 770.60 da za a yi amfani da su wajen ƙarfafa tsaro domin daƙile duk wata barazanar tsaro a ƙasar nan.

Najeriya na tsakiyar matsalolin tsaro a dukkan faɗin ƙasar nan. Ita ce ƙasar da aka fi yin hare-haren ta’addanci a Afrika. Kuma a Najeriya ‘yan bindiga na ci gaba da kisa, ƙwacen dukiyoyi da garkuwa da jama’a barkatai a kowace rana.

A kudancin ƙasar kuwa tsagerun IPOB na ƙara matsa-lambar neman ɓallewa daga Najeriya, domin su kafa ‘Biafra’.

A yankin kudu maso gabas, masu neman kafa Yoruba Nation sai ƙara yunƙurowa su ke yi.

Share.

game da Author