Gwamnar Jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace zai fara aiwatar da shawarwarin da kwamitin tsohon sufeton ƴan sanda Muhammad Abubakar ya baiwa gwamnatinsa kan cewa ya cire wasu sarakuna da ake zarginsu da alaka da Ƴan bindiga.
A jawabi na musamman da gwamnan yayi a ranar dimokaraɗiya ta June 12 yace ya kado matuka dangane da cigaban hare hare na ta’addanci da yan bindiga suke cigaba da kaiwa ciki harda na ranar Juma’a da aka a Kauyen Kadawa, a karamar HUKUMAR Zurmi.
Karanta cikkakken bayanin gwamna Matawalle nan kasa.
Yan Uwana al’ummar jihar Zamfara, na yanke shawarar yi ma ku jawabin a wannan marece, cikin kaduwa da jimami, bisa la’akari da yadda hare-haren yan’ta’adda ke kara ta’azzara a wasu sassan wannan jiha. Kamar yadda kuka sani, na baya bayan nan shi ne harin da aka kai a kauyen Kadawa na karamar hukumar Zurmi. Rahotannin da muka samu sun tabbatar da kashe mutane da dama.
2. Na yi tsananin bakin cikin faruwar wannan aikin dabbanci da wasu matsorata ke aikatawa. Cikin alhini, amadadin iyali na da daukacin al’ummar wannan jiha, ina mika sakon ta’aziyya akan wannan kisan gilla. Muna jajantawa dukkanin iyalan da suka rasa yan’uwansu a duk fadin wannan jiha a sanadiyyar ayyukan ta’addanci.
3. Muna rokon Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya kuma ya ba iyalin su hakurin jure wannan rashi. Muna kuma rokon Allah ya isar ma su.
4. A yayin da nake yi ma ku ta’aziyya, ina mai jaddada ma ku cewa zamu ci gaba da aiki tukuru domin ƙalubalantar waɗannan marasa imani. Rashin son zaman lafiyar su ya tabbar muna da cewa babu wani matakin da ya cancanci mu dauka akan su fiye da na amfani da karfin hukuma.
5. A ƴan kwanakin nan, mun fahimci cewa hare haren ta’addanci sun karu matuka a sassa daban daban na jihar nan. Waɗannan ƴan ta’addan basu la’akari da kiyayewa daga hakkin kashe kananan yara, mata, da tsofaffi. Hakika rashin imanin su ya kai matuka. Kuma muna sane da cewa wadannan hare hare sun yi sanadiyyar raba iyalai da dama daga matsugunnan su. Wannan abin alhini ne da damuwa ga gwamnati.
6. Kamar yadda al’ummar jihar Zamfara suka sani, tun shigowar wannan gwamnati tamu mun yi iyakacin kokarin mu domin ganin mun ci galaba akan wadannan makiya zaman lafiya. Mun samu nasarori da dama, amma abun bakin ciki shi ne a ‘yan kwanakin nan lamarin ya sauya sanadiyyar ayukan wadansu fandararru a sassan jihar nan. Kuma mun fahimci cewa akwai wasu mararsa kishin kasa wadanda burin su shi ne tarwatsa jihar domin biyan bukatun kan su. Ina kira ga al’umma su ci gaba da addu’o’i domin Allah ya tona asirin wadannan kangararru da kuma ma su taimaka ma su.
7. Ina tabbatar ma al’aummar wannan jiha cewa ba zamu yi kasa a gwiwa ba wajen yakin waɗannan ɓata gari. Kuma a wannan yaki da muke yi da ta’addanci, gwamnatin mu ta dauki matakin ba sani ba sabo. Duk wanda aka samu da hannu za’a daukin matakin da ya dace akan shi komi girman matsayin shi. Irin wadannan matakai su ne irin wadanda muka fara dauka akan manyan sarakuna kamar na Maru, Dansadu, da kuma na na baya bayan nan Sarkin Zurmi, bayan aukuwar lamrin da ya wakana a jiya.
8. Haka Zalika, gwamnatin mu zata fara aiwatar da shawarwarin dake kumshe a cikin rahoton kwamitin tsohon babban sufetan ‘yan sanda, MD Abubkar. Idan al’umma zasu tuna, a lokacin da na ke karbar rahoton kwaminitin a ranar 11 ga watan Oktoba 2019, na tabbatar wa da al’umma cewa zamu yi amfani da wasu daga cikin shawarwarin kwamitin domin kai karshen wannan matsala wadda taki ci taki cinyewa, wadda muka gada.
9. Ina son in yi amfani da wannan dama damin jaddada kira na ga al’ummar jiha na cewa da su tashi tsaye domin kare garuruwan su idan an kawo ma su harin ta’addanci. Duk wanda yace gwamnati ta ce kada su kare kansu karya yake yi ma wannan gwamnanti. Abun da kawai muka hana shi ne yawo da makamai a kasuwannni da takalar fitina.
10. Ina kira ga al’umma da su cigaba da sa idanu ga duk wata bakuwar ijjiya da kuma ba jami’an tsaro hadin kai a wannan gagarumin yaki.
11. Muna sane da cewa jami’an tasro suna wasu sabbin tsare tsare domin kai karshen wadannan mummunan ‘yan’taadda mara sa imani.
12. Daga karshe ina rokon Allah subhanahu wata’ala da ya dawo muna da zaman lafiya a wannan jiha.
13. Nagode.