Matawalle ya kori shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, sakataren gwamnati har da kwamishinonin jihar

0

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle kori kusan duka wani babban jami’an gwamnati da ke shugabantar hukuma ko ma’aikata a jihar.

A sanarwar haka da ta fito daga ofishin kakakin gwamnan, Bappa Zailani, ranar Talata, gwamna Matawalle ya umarci duka wani shugaban hukumar gwamnatin jihar ya mika ragamar shugabancim wannan hukuma ga babban darektan ma’aikatar sa.

Wannan kora bai bar kusan kowa ba domin ya faro ne tun daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnan jihar, zuwa sakataten gwamnatin jihar ya gangara har kwamishinoni sai kuma shugabannin hukumomin gwamnatin jihar na Zamfara.

Sanarwar ta ce kwamishina daya ne kacal e kawai ba a wancakalar ba, kwamishin Tsaro da Harkokin cikin gida, Mohammed Tsafe.

Share.

game da Author