Mata ta kashe mijinta da taɓarya a Jigawa

0

Ƴan Sanda a Jigawa na bincikar wata mata mai suna Hadiza Musa da zargin kashe mijinta da taɓarya a karamar hukumar Kazaure dake a Jihar Jigawa

Jami’i Mai-magana da yawun Ƴan Sanda a Jigawa, Lawan Adam, ya shaidawa wakilan gidajen Jaridu cewa matar yar shekara , 25, mazauniyar ƙauyen Maradawa dake yankin Kazaure ta doke mijinta nata ne da tabarya a ka, daga bisani rai yayi halinsa.

Ƴan Sanda sun ce hakan ya faru ne a ranar 17th June 2021 kuma sun kama wacce ake zargi bayan wani mai suna Usman Mai-rago, Dan Shekara 70 ya kawo korafi ofishin Yan Sanda.

Yan Sandan sun bayyana sunan mamacin da Isah Muhammad, Ɗan Shekara 50, ya rasu a lokacin da ake masa jinya a babban asibitin garin kazaure.

An fara binciken lamarin kafin daga baya a gurfanar da mai laifi a gaban alkali, inji kakakin ƴan Sanda Malam Adam

Share.

game da Author