MANOMA DA MASU SAFARAR ALBASA SUN FUSATA: Mun daina kai albasa dukkan kudancin Najeriya, sai an biya mu diyyar asarar naira biliyan 4.5

0

Kungiyar Manoma da Masu Safarar Albasa na Najeriya sun yanke hulɗa da kakaf jihohin ƙasar nan, har sai an biya su diyyar asarar naira biliyan 4.5 da su ka yi a hare-hare daban-daban da aka riƙa kai masu a jihohin ƙasar nan.

“Daga ranar Litinin 7 Ga Yuni, mun yanke shawarar babu wata mota ko wani ɗan kasuwa da zai sake kai albasa kowace jiha a kudancin ƙasar nan, har sai gwamnati ta biya su diyyar ɗimbin asarar da mu ka yi sandiyyar hare-haren da aka riƙa kai wa ‘yan kasuwar mu a jihohin kudu daban-daban.”

Haka dai Shugaban Kungiyar Manoma da Masu Safarar Albasa (OPMAN), Aliyu Isa ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi a Sokoto.

“An kashe mana mutane da yawa, an ƙone mana tirela 30, ƙananan motoci 9, an ƙone mana shaguna 50, an lalata ko sace mana buhunan albasa 10,000, banda ma asarar sauran kadarori kuma.”

Aliyu Isa ya bayyana sunayen garuruwan da ya ce an kai masu hare-hare da su ka haɗa da Aba a jihar Abia, Shasa a Jihar Oyo sai kuma Mbaise a Jihar Imo.

“Lokacin da aka yi rikicin #EndSARS an biya wasu da dama diyyar asarar da su ka yi, amma mu da ya ke an raina mu, ko kallon arziki ba a yi mana ba.”

“A Shasa an kashe mana mutum 27, an ƙona tirela biyar, an lalata buhunan albasa 5,600, kuma an ƙona ƙananan motoci 12.

“Cikin watan Fabrairu kuma a Jihar Imo an kai mana hari, an ƙona tireloli biyu makare da kaya za su kai na naira miliyan 13.”

Aliyu ya ce ko dai a biya su diyya ko kuma su daina kai albasa a kudancin ƙasar nan.

A ƙarshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su farka su rika kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sannan kuma ya yi kira ga ƙabilun kudu su rungumi Hausawa domin a yi zaman lafiya da juna.

Share.

game da Author