Malejin tsadar rayuwa ya ɗan yi ƙasa, amma kayan abinci ba su sauka ba – NBS

0

Hukumar Ƙididigar Alƙaluman Bayanai ta Najeriya (NBS), wadda mallakin Gwamnatin Tarayya ce, ta shaida cewa malejin tsadar rayuwa ya yi ƙasa tsawon watanni biyu a jere, daga kashi 18.12 bisa 100 a watan Afrilu, yanzu kuma ƙididdiga ta nuna ya ƙara yin ƙasa zuwa 17.93 a cikin watan Yuni, ɗin da ya gabata.

NBS ta fitar da jadawalin farashin tsadar kayan abinci a ranar Talata ɗin nan, wanda ake aunawa da Gejin Farashin Kayan Masarufi na Yau da Kullum wato ‘Consumer Price Index’ (CPI).

Sai dai kuma duk da haka ƙididdigar ta nuna har yanzu har yanzu farashin kayan abinci sai ma ƙaruwa ya ke yi, amma ɗai idan mutum ya da farashin watan Afrilu, zai ga an ɗan samu rangwame ko da ƙanƙanen kuɗi ne..

Farashin kayan abinci dai a tsadar watan Mayu ya tsaya a kashi 22.28, amma a watan Afrilu ya dangwale kwano har kashi 22.72.

Tun daga lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya rufe kan iyakokin Najeriya ake shan ɗan karen tsadar kayan abinci da tsadar rayuwar kan ta.

Matsalar tsaro ta ƙara haifar da tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci. Sai kuma karyewar darajar naira wadda a kullum sai Dalar Amurka ta yi mata dukan tsiya, imma a farashin gwamnati ko farashin ‘yan kasuwar tsaye.

Shi da kansa Buhari ya bayyana cewa “gaskiya ban gamsu da matsayin tattalin arzikin Najeriya ba.”

A karon farko bayan shekaru shida a kan mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana rashin gamsuwar sa da yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Buhari ya bayyana haka a wata tattaunawa da Gidan Talbijin na Kasa, NTA ya yi da shi a ranar Alhamis da dare.

Shugaba Buhari ya ce a gaskiya ya yi matukar damuwa da halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga.

Sai dai kuma ya ƙara shan alwashin cewa gwamnatin sa za ta tayar da komaɗar da tattalin arzikin Najeriya ya samu sakamakon kutufo ɗin da ya sha daga matsaloli da ƙalubale daban-daban.

“Gaskiya ban gamsu da tattalin arzikin Najeriya ba.” Haka Buhari ya bayyana matsayin amsar tambayar da aka yi masa kan tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai kuma ya ce gwamnatin sa na ƙoƙarin ganin baƙi na ƙara zuba jari cikin ƙasar nan daga ƙasashen waje.

Buhari wanda ya hau mulki cikin 2015 bisa alƙawarin kawar da rashawa da cin hanci, matsalar tsaro da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa, a yanzu kuma bayan shekaru shida ya gamsu da cewa har yau tattalin arzikin Najeriya ki dai tafiyar-kura ya ke yi, ko kuma tsalle ya ke ta yi, ba gudu ba.

Haka a ranar Juma’a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talbijin na Arise TV, Buhari ya bayyana cewa “daƙile cin hanci da rashawa a ƙarƙashin gwamnatin dimokuraɗiyya, abu ne mai matuƙar wahala.”

PREMIUM TIMES ta buga sharhin yadda Buhari ya shafe shekaru shida kan mulki, amma ya kasa samun nasara a shika-shikan tattalin arzikin ƙasa guda bakwai.

Buhari ya ƙara haifar da tsadar rayuwa maimakon a samu sauƙi, farashin kayan abinci da na kayan masarufi a kullum sai tashi sama su ke yi. Ga matsalar taɓarɓarewar darajar Naira, ga rashin aikin yi ga kuma rashin bunƙasar noma, duk kuwa da ɗimbin biliyoyin nairorin da ake bayarwa ramce ga manoma.

Share.

game da Author