Ma su fadin wai ba na yi wa ƴan bindiga yankin Arewa ragargazar da ake wa ƴan kudu saboda son kai, ba su yi min adalci ba – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa masu sukar sa wai ba ya ragargazar ƴan bindigan yankin Arewa kamar yadda ya ke wa na kudu wato ƴan ESN saboda son kai ba su yi masa adalci ba.

” Ina son masu faɗin irin waɗannan maganganu su je su tambayi gwamnonin Sokoto, Kebbi da Zamfara su gaya musu yadda mu keyi a wadannan yankuna. Amma wai ina nuna son kai bai ma ta so ba.

” Ba za mu ɗaga wa kowani kangararre kafa ba, abinda akwai shi ne Najeriya na da manya-manyan dazuka a kasar nan.

Bincike da PREMIUM TIMES ta yi sun nuna cewa tabbas akwai rundunoni daban daban da aka kakkafa domin yaki da ƴan bindiga a yankin Arewa ba kamar yadda masu ƙorafi ke faɗi ba.

Game da kalaman da yayi kan ƴan Biafra cewa za a bi da su ta irin hanyar da za su fi ganewa, shugaba Buhari yayi karin haske akai.

” Abinda nake nufi shine, yanzu tsakani da Allah ace wai sai kawai a yi gungu a afkawa ofishin ƴan sanda, a kashe ƴan sandan, a kona ofishin sannan a kwashe makaman su a yi awon gaba da su. Yaya kuke so ayi da irin waɗannan mutane. Shi ke nan sai a zura musu ido? Babu wata kasa a duniya da zata yi haka.

“Ku duba jihar Legas a lokacin zanga-zangar EndSars, haka kawai mazu zanga-zanga suka afka wa tarin manyan motoci da gwamnati ta siya har 200 suka babbake su. Suka afka firsinoni suka fasa su suka saki daurarru. Ina amfanin haka.

A karshe Buhari ya ce idan aka kama irin wadannan kangararru, za a kai su kuto sannan su yi zaman gidan kaso kamar yadda doka ta ce.

Share.

game da Author