Jam’iyyar APC ta maida wa PDP da martani cewa da ta yi wai gwamnonin APC na shirya gagarimin maguɗi a 2023.
PDP ta ce zata garzaya Kotu domin ganin wannan kujera ta gwamnan Zamfara ta dawo hannun jam’iyyar kamar yadda kotun ƙoli ta yanke.
Sai dai jam’iyyar APC ta maida martani cewa Lemar PDP ce ke yoyo, duk ta ɓuɓɓule, shi ne yasa da gwamnonin da ƴan majalisun duk suke ta tsiyayowa kasa mukuma muna tattara su.
” Ɓaraka ce aka samu a jam’iyyar kuma ta kasa dinke su, shine yasa gaba ɗaya jam’iyyar ta faɗa cikin ruɗani har ya kai ga kowa yana kama gabar sa.
” Kusan duka waɗanda suka dawo APC, a baya ƴan PDP ne. Dukkan su kuma sun sha fama da murɗiyar zaɓe. Amma a gaya mana inda muka taba murɗe wa wani zaɓe a kasar nan.
Abin da aka gano yanzu shine ashe haɗin kan PDP ya na da nasaba da warwason da suke yi a asusun gwamnati. Yanzu da babu yadda za su riƙa gabzan kuɗin gwamnati duk gashi sai kame-kame suke yi, Lemar ma ta huhhuje gab taje da ta karye, shikenan.
Canja sheƙar da gwamnan Zamfara Bello Matawalle yayi, ya yi matuƙar tada wa jam’iyyar PDP hankali, domin a cikin watanni shida, gwamnonin jam’iyyar su uku tare da ɗimbin illahirin magiya bayan su da ƴan majalisun su kaf suka bisu jam’iyyar APC.
Discussion about this post