Tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya bayyana cewa yana maraba da shigan gwamnan jihar Bello Matawalle jam’iyyar APC.
AbdulAziz wanda ya gana da ƴaƴan jam’iyyar APC na jihar Zamfara a garin Kaduna ya ce suna maraba da gwamnan.
” Fata na shine idan ya shigo APC a samu haɗin kai da ci gaba a jam’iyyar. Mu dai ba zamuyi komai ba ba tare da mutanen mu ba. Komai sai mun gaya musu mun ne mi shawarar ƴan jam’iyya.
A na sa ran gwamna Matawalle zai bayyana canja sheka daga PDP zuwa APC ranar Talata.
Idan ba a manta ba Matawalle ya daɗe yana nuna alamun zai canja sheka zuwa APC amma amma kuma sai abin ya shashance.
Ko a wannan karon ma sai da ya musanta cewa zai koma APC.