Yayin da tuni har Faruk Lawan ya fara zaman ɗaurin shekara bakwai da Alƙalin Babbar Kotun Abuja, Angela Otaluka ta yi masa a ranar Lahadi, jama’a sun cika da mamakin jin yadda aka ɗauke mai karɓar toshiyar bakin dala 500,000, amma ba a ɗaure Femi Otedola, wanda ya bayar da cin hancin kuɗaɗen.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bi wa masu karatu diddigi shari’ar, tun ma daga farkon lamarin, zuwa ranar da aka bada kuɗaɗen da kuma dalilin ƙin ɗauke Otedola.
1. Mai Shari’a Angela ta yi amfani da shaidar da Femi Otedola ya bayar, wanda shi ne ya bayar da cin hancin tun a cikin 2012.
2. Yayin shari’ar, da mai karɓa da mai bayarwa duk sun yarda cewa dala 500,000 ta fita daga hannun wannan zuwa hannun wancan.
3. Amma Femi Otedola ya ce wa Kotu ya bayar da kuɗin ne domin su zama shaidar kama Farouk Lawan, saboda ya nemi ya ba shi cin hanci.
4. Shi ma Farouk Lawan cewa ya yi ya karɓi kuɗin ne a matsayin shaida da hujja cewa Otedola ya ba shi cin hanci, domin a cire sunan kamfanin sa daga kamfanonin mai waɗanda sunayen su ke cikin waɗanda aka samu da harƙallar kuɗin tallafin mai a 2012.
5. Mai Shari’a Angela ta yarda da hujjar Otedola, ta ƙi yarda da hujjar Farouk Lawan. Ga dalilan ta:
6. Gurungunɗumar ta samo asali ne daga wani kwamiti da Majalisar Tarayya ta kafa cikin 2012, domin a bankaɗo kamfanonin da su ka yi harƙalla da badaƙalar kuɗaɗen tallafin man fetur.
7. Farouk Lawan shi ne Shugaban Kwamitin Bincike a lokacin.
8. Kamfanin mai na biloniya Otedola, wato Zenon Oil and Gas, an zarge shi da karɓar canjin kuɗaɗen arha takyaf a CBN, har dala miliyan 230, domin shigo da fetur cikin Najeriya daga waje. Amma ya yi mirsisi bai shigo da fetur ɗin ba.
9. A tuhumar da aka yi wa Farouk Lawan, Gwamnatin Tarayya ce ke ƙarar sa a kan zargin ya nemi toshiyar baki ta dala miliyan 3, domin a cire sunan Zenon Oil and Gas daga jerin kamfanonin da su ka yi harƙallar.
10. Farouk Lawan ya karɓi dala 500,000 daga hannun Femi Otedola, bisa sharaɗin za a cika masa sauran dala miliyan 2.5.
11. Otedola ya shaida wa kotu cewa kamfanonin sa ko ɗaya ba su shiga cikin harƙallar kuɗaɗen tallafin man fetur ɗin ba.
12. Otedola ya ce ƙiri-ƙiri Farouk Lawan ya tsarma sunan kamfanin sa cikin ‘yan harƙallar, don kawai ya tatsi kudi a hannun sa.
13. Mai gabatar da ƙara, Babban Lauya Adegboyega Awomolo, ya shaida wa kotu irin yadda aka riƙa yin tsallen-gada da Farouk Lawan, wanda ya nemi wanke kamfanin Zenon Oil.
An Gina Wa Farouk Lawan Tarko Ya Rufta Ciki:
14. “Daga nan sai ni mai gabatar da ƙara na tuntubi DSS a lokacin da Lawan ya nemi na ba shi cin hancin dala miliyan 3.
15. Su kuma DSS su ka ba ni daloli 500,000, kuma duk su ka yi masu shaidar alama. Su ka haɗa ni da jami’ai shida da wata na’ura wadda ita mu ka yi amfani duk mu ka yi rikodin din abin da ya faru.” Inji Otedola.
16. A lokacin shari’ar, mai gabatar da ƙara ya kunna bidiyon da aka nuno Farouk Lawan ya na karɓar wata sunƙin ambulan, wadda aka ce ta ƙunshi dala 500,000 a cikin ta da DSS su ka ba Otedola, shi kuma ya bai wa Farouk Lawan.
17. Otedola ya ce Lawan ya je ya cire sunan kamfanin sa daga sunayen kamfanin da aka kama da harƙallar kuɗin tallafin mai. Bayan ya karɓi dala 500,000 kenan.”
18. “Bayan an bai wa Lawan kuɗaɗen da safiyar ranar 24 Ga Afrilu, 2012, sai ya tafi ya cire sunan Zenon Oil daga sunayen kamfanonin da su ka ce sun kama da laifi.” Inji Otedola.
Ta Bakin Farouk Lawan:
19. Lawan ya ce ya karɓi kuɗi ne a hannun Otedola a matsayin hujjar yadda kamfanonin da aka kama da laifi su ka riƙa ƙoƙarin ba shi cin hanci shi da ‘yan kwamitin sa, domin a cire sunayen su daga masu laifi.
Zarge Mugun Ƙulli:
20. Farouk Lawan bai sani ba ashe haɗa baki aka yi da Sakataren Kwamiti, Boniface Emenalo, wanda Farouk Lawan ya ba dala 100,000 daga cikin dala 500,000 ɗin da ya karɓa a hannun Otedola.
21. Emenalo ya gabatar da kuɗin a kotu, a matsayin hujjar cewa Lawan ya kasafta cin hancin da ya karɓo. Ba wai hujjar kama Otedola ya karɓa daga hannun sa ba.
22. Otedola ya ƙara jaddada wa kotu cewa kawai ya tuntuɓi DSS don su kama Farouk Lawan dumu-dumu ne. Saboda ya yi masa sharri ya tsarma sunan kamfanin sa cikin harƙallar, alhali kamfanin sa bai shiga harƙallar ba.
23. Shi ya tambaya. Idan bai tambaya ba, me ya sa da aka ba shi ya karɓa, har ya ke jiran cikon dala miliyan 2.5? Kuma waɗanda ya karɓa ɗin ya kasafta ya ba sakataren kwamiti dala 100,000.” Inji Otedola.
24. Mai Shari’a ya ɗora laifi kan Lawan, domin da ya karɓi kuɗin kasaftawa ya yi bai kai rahoto ga jami’an tsaro ba.
25. Kotu ta kara kama Farouk Lawan da laifi, saboda ya na karɓar kuɗin, garzayawa Majalisar Tarayya ya yi ya soke sunan Zenon Oil.
ABIN LURA: Kuɗin Gwamnatin Tarayya ne Farouk Lawan ya karɓa daga hannun Otedola, waɗanda DSS su ka ba shi, domin a kama Lawan. Ba ainihin kuɗin Otedola ba ne na aljihun sa.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda kotu ta kama Faruk Lawan da laifin karɓar toshiyar bakin dala 500,000, ta ɗaure shi shekara bakwai.
Shari’ar da aka shafe shekaru tara ana tuhumar tsohon Dan Majalisar Tarayya, Farouk Lawan da laifin karɓar toshiyar bakin dala 500,000 daga hannun hamshaƙin attajiri kuma babban dillalin fetur, ta zo ƙarshe, domin an ɗaure shi shekaru bakwai a kurkuku.
A yau Talata ne aka yanke wa Lawan hukunci a ƙarƙashin Babban Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja. To sai dai kuma yayin da wanda ake tuhuma ya tsaya kai da fata cewa bai karɓi cin hancin ba, Mai Shari’a Angela Otaluka ta yi watsi da roƙon da Lawan ya yi.
Ana tuhumar Lawan da laifin karɓar toshiyar bakin dala 500,000 daga hannun Femi Otedola a bisa yarjejeniyar cewa za a cire sunan kamfanin sa daga cikin kamfanonin da Kwamitin Majalisa Mai Binciken Harƙallar Kuɗaɗen Tallafin Fetur, ya kama da laifi dumu-dumu.
Lawan an zarge shi da laifin neman cin hancin dala miliyan 3, a madadin shi Shugaban Kwamiti da kuma sauran mambobin kwamiti.
Otedola ya shaida wa duniya cewa ya ɗana wa Lawan tarko, kuma ya kama shi, domin kyamara ta nuno lokacin da ake ba shi kuɗaɗen, haka an nuno lokacin da ya ke karɓar.
Otedola ya ce ya fara ba shi dala 500,000 ce, saura dala miliyan 2.5 kenan.
An maka kotu tun cikin 2012, inda aka shafe shekaru tara kenan, ana ƙaƙudubar shari’a.
Bayan shari’a ta yi nisa, Lawan ya garzaya Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, inda ya nemi kotun ta dakatar da Babbar Kotun Abuja, domin a cewar sa bai karɓi toshiyar bakin ba.
Kotun dai ta ce ya na da tuhumar da zai amsa, don haka a je a ci gaba da shari’a.
An shirya zartas da hukunci a kan sa tun cikin makon da ya gabata. Amma haka bai yiwu ba, sai Mai Shari’a ta tsaida ranar yau Talata.
Yayin da aka zauna yau Talata, Mai Shari’a ta share fagen yanke masa hukunci, yayin da ta ƙi karɓar uzurin sa cewa bai aikata laifin da ake tuhumar sa ba.
Kafin Mai Shari’a Otaluka dai alƙalai biyu sun saurari ƙarar a shekarun baya. Na farko ƙarin girma aka yi masa zuwa Babbar Kotun Tarayya.
Mai Shari’a ta biyu kuma janye hannun ta ta yi a shari’ar, saboda Lawan ya zarge ta da nuna masa bambanci da rashin adalci.