Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS) sun yi wa Tiwita tofin tsinuwar daina amfani da ita

0

Kungiyar Dalibai ta Najeriya (MSS), ta umarci dukkan rassan ta na Kananan Hukumomi, Manyan Makarantu da Jami’o’i na Jihar Lagos su dakatar da yin amfani da Tiwita wajen isar da sakonni da sauran ayyukan da su ka jibinci kungiya.

Shugaban Kungiyar na Jihar Lagos, Miftahuddeen Thanni ne ya sanar da haka a ranar Talata a Lagos, cikin wata sanarwa da ya fitar.

Wannan umarni ya fito ne biyo bayan dakatar da Tiwita da Gwamnatin Tarayya ta yi.

MSSN ta Jihar Lagos ta ce, “yayin da mu ka tabbatar kuma mu ka hakkake cewa Gwamnatin Tarayya ba ta kokari wajen samar da tsaro da wasu bangarorin da ta kasa, duk da haka bijire wa umarnin Gwamnati kan dakatar da Tiwita bai kamata ba.

“Mun san cewa a karkashin wanann gwamnatin ma ana tauye wa Musulmi ‘yanci sosai, musamman ‘yancin amfani da hijabi, amma dakatar da Tiwita abu ne mai kyau da Gwamnatin Tarayya ta yi.

“Tabbas duk kungiyar da ta san abin da ta ke yi, za ta yi fadutika da nan ‘yancin fadin ra’ayi. Amma kuma hadin kan Najeriya ya na gaba da komai.”

Ya kara da cewa duk da za a iya jan-kunnen Tiwita ba tare da sai an dakatar da ita ba, “Amma kuma rashin adalcin da Tiwita ta rika yi wajen kan waau abubuwa na laifuka da ‘yan #EndSARS da IPOB su ka rika yi, wato lalata dukiyoyi, bai kamata ta kauda kai a kan su ba.

“Don haka kuma mu na kira ga Shugaban Kasa ya gaggauta yi wa matsalar tsaro dirar-mikiya, kamar yadda ya yi wa Tiwita cikin kankanin lokaci.”

Share.

game da Author