Babbar Kotun Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta haramta wa Gwamnatin Najeriya kamawa, kullewa ko hukunta wani ko wasu ƙungiyoyi ko kafafen yaɗa labaran da su ka yi amfani da Tiwita a ƙasar nan.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Ƙungiyar SERAP tare wasu mutum 176 su ka maka Gwamnatin Najeriya kotu, su na masu ƙarfin cewa dakatar da amfani da Tiwita tauye masu haƙƙi ne.
Kotun ta ECOWAS dai ta yanke hukuncin cewa kada Gwamnatin Najeriya ta kama ko hukunta wani ko wasu ko jarida, gidan talabijin, mujallu, radiyo, ko shafukan sada zumunci na soshiyal midiya, har sai an ji hukuncin da kotun za ta yanke tukunna.
Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ne ya sanar da wannan nasara da su ka yi a kotu, a yau Talata.
Lauyan SERAP Femi Falala, ya yi bayanin da ya bayyana cewa:
“Gaskiya babban abin kunya ne ga Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar hukuntawa da kuma tuhumar wanda ya yi amfani da Tiwita a matsayin wanda ya ci amanar ƙasa, domin tun 1983 kotu ta haramta tare da soke irin wannan hukunci, a shari’ar Arthur Nwankwo da Gwamnatin Tarayya.”
PREMIUM TIMES kuma ta buga labarin yadda wasu ƙungiyoyi biyar da ‘yan jarida huɗu sun maka gwamnatin Buhari gaban Kotun ECOWAS.
Wasu ƙungiyoyin sa-kai da kare haƙƙin jama’a, sun maka Gwamnatin Najeriya a Kotun Ƙasashen Afrika ta Yamma mai hedikwata a Abuja, inda su ka nemi kotun ta tirsasa wa Gwamnatin Shugaba Buhari ta buɗe Tiwita daga dakatarwar da ta yi mata.
Ƙungiyoyin waɗanda su ka garzaya kotun tare da wasu ‘yan jarida huɗu, sun kuma nemi gwamnati ta biya su diyyar danne masu haƙƙi, tauye masu ‘yamci da kuma haddasa masu kasa isar da saƙonni ko karɓar saƙonni ta Tiwita da gwamnatin ta yi.
Ƙungiyoyin sun haɗa da MPA, PIN, PTCIJ, IPC da kuma TICD, tare da ‘yan jaridar da su ka haɗa da David Hundeyin, Samuel Ogundipe, Blessing Oladunjoye da Nwakambi Zakari, sun ce sun ɗibga asara mai yawa a tsawon kwanakin da su ka yi ba su yi amfani da Tiwita ba, tun daga ranar 4 Ga Yuni, 2021.
Bugu da ƙari sun ce hukuncin dakatar da Tiwita da Najeriya ta ɗauka, ya kauce daga yarjejeniyar ƙasashen Afirka ta Yamma, a ƙarƙashin ECOWAS, wadda Najeriya ɗin na cikin ƙasashen da su ka ƙalla yarjejeniyar.
Sun maka Gwamnatin Najeriya gaban kotun ne tare da goyon bayan wata riƙaƙƙiyar Ƙungiyar Kare Haƙƙi da Muradun Kafafen Yaɗa Labarai da ke Landan, mai suna Media Defence.
‘Media Defence’ ta shahara wajen bai wa ‘yan jarida, ‘yan ƙasa da kafafen yaɗa labarai masu zaman kan su kariya a kotu da kuma neman masu haƙƙin su.
Lauya Mojirayo Nkanga ne ya shigar da ƙarar a madadin ɓangarorin masu masu ƙarar biyu.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ga kwafen takardun shigar da ƙarar mai lamba ECW/CCJ/APP/29/22 masu ɗauke da shafukan dogon Turanci har shafi 73.
Wannan ƙarar dai daban ta ke da wadda SERAP ta kai. Kotu ba ta kai ga sa ranar fara sauraren ƙarar ba tukunna.