Ku koma aiki ‘ko cefane ya gagare ku’ idan mun hana ku albashi – Gargadin Gwamnati ga ma’aikatan kotu da na majalisu

0

Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan ma’aikatan kotuna da na Majalisun Dokokin Jihohi su gaggauta yanke yajin aikin da su ke yi tsawon watanni biyu, su koma bakin aikin su.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Ngige ya yi masu gargadin cewa idan ba su koma aiki ba, to Gwamnatin Tarayya za ta tilasta wa kan ta yin amfani da dokar rike albashin wanda bai je aiki ba, a hana shi tsawon watannin da ya yi fashi bai je aikin ba.

Wannan gargadi dai na nufin gwamnati ta kasa shawo kan lamarin, abin da kawai ya rage shi ne a yi baram-baram tsakanin ta da kungiyoyin JUSUN da ta Ma’aikatan Majalisun Jihohi.

“Ma’aikatar Kwadago ba za ta so a tura ta har ta kai bango ta rike albashin ma’aikata, bayan an rigaya an soma cin nasarar tattaunawar da aka fara tun daga ranar 6 Ga Mayu.”

Wannan sanarwa dai Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Kwadago, Charles Akpan ne ya sa mata hannu, a madadin Minista Ngige.

Ngige ya nuna matukar damuwa ganin yadda kotunan kasar nan da Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya kakaf ke kulle ba su aiki tsawon watanni biyu, ba tare da wani dalilin kulle su ba.”

“Gwamnatin Tarayya ta damu ganin yadda bangarorin JUSUN/PASAN da Kungiyar Gwamnoni su ka kasa cika alkawurran da su ka cimma a yarjejeniyar baya-bayan nan da aka kulla a gaban Kwamitin Shugaban Kasa, wadda a wurin taron har Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa (NLC) ya halarta.”

Daga nan ya roki su gaggauta komawa aiki, domin rufe kotunan Najeriya ya damalmala matsalar shari’u da wasu bangarorin ayyukan da su ka jibinci tsaro ko kula da masu aikata manya da kananan laifuka.

Share.

game da Author