Gwamnatin tarayya ta saka kasar Afrika ta Kudu a jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can sauka a Najeriya saboda yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisan fard-daya wato ‘Delta Variants’.
Gwamnati ta kuma ce sai fasinjoji ‘yan Najeriya da dawo daga kasar sun kiyaye dokokin Korona da aka saka kafin a bari su shiga garuruwan kasar nan.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona PSC Boss Mustapha ya sanar da haka ranar Litini.
Mustapha ya ce gwamnati ta yanke wannan hukunci ne saboda ftinar da ta hango na kokarin dannowa Najeriya.
Zuwa yanzu mutum 100,000 sun kamu da sabuwan sumfurin Korona a cikin makon da ya gabata sannan a cikin awa 24 an samu karin mutum 20,000 da suka kamu a Afrika ta Kudu.
Idan ba a manta ba ranar 1 ga Mayu ne Kwamitin PSC ya sanar da sabuwar dokar da gwamnati ta kafa cewa duk fasinjan da zai sauka Najeriya daga Indiya ko Brazil ko Turkiyya, tilas ne a killace shi tsawon kwanaki bakwai, kafin a bar shi ya shiga cikin garuruwan Najeriya.
Bijiro da wannan doka ya biyo bayan bullar sabuwar samfurin cutar korona mai yawan kisan mutane birjik musamman a Indiya da Brazil.
Bisa ga sakamakon gwajin korona da ‘Worldometers’ ta fitar cikin kwananan ya nuna cewa mutum miliyan 5.4 sun kamu sannan mutum 145,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar a Nahiyar Afrika