Ko gwamnatin Najeriya ta janye dakatar da Tiwita ko mu hadu a Kotu – Kungiyar Lauyoyin Najeriya

0

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya NBA, Olumide Akpata, ya kalubalanci gwamnatin Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta gaggauta janye dakatar da Tiwita da ta yi ko su hadu da ita a kotu.

Idan ba a manta ba Kungiyar SERAP ce ta fara bayyana rashin jin dadin kan dakatar da Tiwita da gwamnatin tarayya ta yi ta ce hana amfani da kafar soshiyal midiya din haramtacce ne, kuma ƙungiyar ta ce za ta gaggauta maka gwamnatin tarayya kotu.

SERAP ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter, ko kuma ta maka ta kotu kai-tsaye.

SERAP a fusace ta kira dakatarwar haramtacciya, kamar yadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.

“Dakatar da twitter a Najeriya tauye wa ‘yan Najeriya ‘yancin faɗar albarkacin bakin su ne da kuma toshe masu wata muhimmiyar kafar samun bayanai da aika saƙonni.

“Wannan dakatarwar wani salo ne aka yi amfani da shi na azabtar da mutane bai-ɗaya a lokaci guda. Hakan ya saba wa tsarin dokokin ƙasa-da-ƙasa.

“Saboda haka mu na kira ga Shugaba Buhari ya gaggauta janye wannan dakatarwar, cikin sa’o’i 48 ko kuma mu da shi mu haɗu a kotu, saboda ya danne haƙƙin jama’a masu tarin yawa.

Ita ma kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta bi sawun SERAP in da ta ce yun haka da gwamnati tayi ya saba wa dokar kasa da ya ba duk dan kasa ikon watayawa da fadin albarkacin bakin sa.

NBA ta ce lallai gwamnati ta gaggauta wannan katoɓara da ta yi na dakatar da Tiwita a Najeriya tun da wuri, ko kuma sai inda karfin su ya kare a Kotu.

A yau Juma’a ce Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana dakatar da twitter daga amfani a Najeriya har sai yadda hali ya yi.

Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Lai, Segun Adeyemi ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin ministan.

Share.

game da Author