KIWON LAFIYA: Kwalera ta kashe mutum 119 a Kano cikin watanni Uku

0

Ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Kano ta bayyana cewa cutar kwalara ta yi ajalin mutum 119 daga ranar 5 ga Maris zuwa ranar 22 ga Yunin 2021.

Ma’aikatar ta kuma ce a tsakanin wannan lokaci mutum 3,290 sun kamu da cutar.

Mataimakin shugaban fannin kula da kiwon lafiyar mutane na ma’aikatar Bashir Lawan ya sanar da haka a zantawa da yayi da PREMIUM TIMES ranar Talata.

Lawan ya ce cutar ta bullo a kananan hukumomi 33 daga cikin kananan hukumomi 44 dake jihar.

Ya ce kananan hukumomin Gaya da Bichi ne suka fi fama da yaduwar cutar.

Lawan ya ce zuwa yanzu mutum 2,996 sun warke sai dai har yanzu akwai mutum 105 dake kwance a asibitocin kananan hukumomi 7 a jihar.

Ya ce wayar da kan mutane kan tsaftace jikinsu da muhallin su su ne muhimman matakan da za abi wajen kawo karshen yaduwar cutar a jihar.

Share.

game da Author