Kungiyar Dattawan Arewa ta nuna kakkausan gargaɗi da bacin rai dangane da kisan ‘yan Arewa mazauna kudancin ƙasar nan, musamman a Kudu maso Gabas da ke yi.
ACF ta ce ya kamata ‘yan kudu su sani cewa wannan mummunar turba da su ka ɗauka, ba za ta haifar wa ƙasar nan baki ɗaya ɗa mai ido ba, domin ya kamata su tuna cewa fa da haka ne Yaƙin Basasa ya barke.
Yaƙin Basasa ya barke tsawon watanni 30, daga 1967 zuwa 1970, bayan kisan shugabanni ‘yan Arewa, su marigayi Abubakar Tafawa Balewa, Sardauna Ahmadu Bello da wasu manyan sojojin Arewa.
Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa, Audu Ogbeh ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya yi tofin-Allah-tsine kan kisan Ahmed Gulak da aka yi a Imo, sannan ya shawarci ‘yan Arewa su ƙaurace wa zuwa jihohin ƙabilar Igbo, sai fa idan tafiyar ta dole ce babu wakilci.
Ogbeh ya tuna yadda Shugabannin Ƙungiyar Masu Hada-hadar Dabbobi da Abinci ta Najeriya (AUFCDN), sun shiga yajin aiki saboda hare-haren da aka riƙa kai masu a kudancin ƙasar nan a lokacin watannin baya.
“Idan kun tuna, Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ce ta lallashi Kungiyar Masu Safarar Abinci da Dabbobi (AUFCDN), ta janye yakin aikin kai abinci jihohin kudu cikin watan Fabrairu, domin yin amanna da ɗayantakar Najeriya dunƙulalliyar ƙasa ɗaya.
“A ranar 30 Ga Mayu, an bindige ɗaya daga cikin shugabannin Arewa a cikin Owerri, kan titi, babban birnin Jihar Imo. Kuma an zargi ‘yan iskan IPOB/ESN ne da aikata wannan kisan-gilla, kamar yadda su ke kan aikatawa, domin neman kafa ƙasar Biafra.
“A kan haka ACF na yin kakkausan gargaɗi ga duk wani ɗan Arewa kada ya niƙi gari ya tunkari Kudu maso Yamma. Idan ma zai je, to a auna mahimancin zuwan bisa sikelin mahimmancin rayuwar sa tukunna.
“Mu na yi wannan gargaɗin ne domin tuna wa jama’a cewa Yaƙin Basasa na 1966 ya samo asali kuma ya barke har tsawon watanni 30 zuwa cikin 1970. Kuma ya haddasa mutuwar dubun dubatar mutane da jefa miliyoyin mutane cikin azabtacciyar walaha, kunci, yunwa da cuce-cuce.”
Daga nan ACP ta yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta kamo dukkan masu hannu a kisan Ahmed Gulak domin a hukunta su daidai irin laifin da su ka aikata.
“Rayukan ‘yan Arewa da na sauran ‘yan Najeriya na da tsada, daga yau ACF ba za ta sake zura ido ko ta gi shiru ba waɗansu tantagaryar ‘yan iska na kashe mutane ba ji ba gani ba.” Inji Audu Ogbe, wanda ya riƙe muƙamin Ministan Harkokin Gona tsakanin 2015 zuwa 2019. A hannun sa Minista Sabo Nanono ya gaji muƙamin.