Jam’iyyar APC a jihar Koros-Ribas ta yo odar daurin tsintsiya har miliyan Uku domin karancin shi da aka samu a kasar har.
Kakakin jam’iyyar Bassey Ita ya bayyana cewa haka ranar litinin a garin Calabar
” Tun bayan tsindima cikin jam’iyyar APC da gwamna Ayade yayi, aka soma samun karancin tsintsiya a jihar. Mutane na ta yin tururuwa zuwa cikin jam’iyyar kuma da yake tsintsiya ne tambarin jam’iyyar duk mai shiga zai so yana maƙale da ita.
” A dalilin haka ya sa muka yi Odar tsintsiya daga kasuwannin kauyuka har ɗauri miliyan uku domin ya wadata ko ina a faɗin jihar.
Ita ya kara da cewa a makon jiya, shugabannin ƙananan hukumomin jihar, da Kansiloli, ƴan majalisa da magoya bayan su kaf suka shigo jam’iyyar. Hakan ya sa tsintsiya ya kare kaf.
A karshe ya jinjina wa mutanen jihar kan irin goyon bayan da suke baiwa gwamnan jihar tun bayn komawarsa jam’iyyar APC.
” Tun bayan komawar gwamna Ayade APC aka fara jin jihar Koros-Ribas a tsare-tsaren gwamnati a tsakiya.
Idan ba a manta ba a cikin watan Afirilu gwamna Ayade ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Shugaban jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mala Buni tare da wasu gwamnoni suka karɓi gwamnan a Ayade a Calabar.