KARANCIN MALAMAI: Ma’aikatan gwamnati 5000 za su koma aji – In ji Ganduje

0

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta mai da ma’aikatan gwamnati 5,000 da suka karanci aikin koyarwa zuwa makarantun jihar.

Kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ya sanar da haka wa manema labarai ranar Lahadi a garin Kano.

Garba ya ce gwamnati za ta yi hakan ne domin karfafa kudirin samar da ilimin boko kyauta a jihar daga yanzu zuwa 2030.

“An kafa kwamiti domin zakulo ma’aikatan da suka yi karatun koyon aikin malunta domin a tura su a jujuwa su ci gaba da karantar da yaran a jihar.

“Gwamnati za ta yi wa wadannan ma’aikata ritaya domin su fara koyarwa a makarantun sakandaren jihar da jami’o’in jihar.

Rahotannin da kwamitin ya gabatar ya nuna cewa akwai ma’aikatan gwamnati 575 da suka yi karatun aikin malunta kuma suna aiki a manyan ma’aikatun jihar sannan akwai wasu ma’aikatan irin haka 3, 712 dake aiki a kananan hukumomin jihar.

Garba ya ce daga cikin wandannan ma’aikata akwai mutum 19 dake da digirin PHD mutum 55 na da digirin digir-gir, mutum 1,100 na da digiri, mutum 2,366 na da NCE sannan 10 na da diploma.

Ya kuma ce sakamakon kwamitin ya nuna cewa an fi samun yawan irin wadannan ma’aikata a kananan hukumomin jihar.

“Ma’aikatan da suke da digirin PHD, digirin digir-gir da digiri za su koma aiki da makarantu sannan wadanda ke da NCE da diploma za su ci gaba da aiki da gwamnati.

Share.

game da Author