Jamin tsaro sun bindige wani ɗalibin Kwalejin Koyan Aikin Malunta dake Jema’a, jihar Kaduna ranar Litini a wajen zanga-zangar karin kudin makarantar.
Ɗaliban kwalejin sun fito yin zanga-zangar nuna rashin amincewar su da karin kuɗin makaranta wanda gwamnatin jihar tayi.
Wasu daga cikin ɗaliban makarantan da suka zanta da wakilin PREMIUM TIMES sun shaida masa cewa ɗaliban sun fito yun zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin kuɗin makaranta wanda gwamnati ta kara.
” A daidai mun taru muna zanga-zangar mu sai jami’an tsaro suka diran mana suka rika harbi a sama. A cikin haka ne aka ɗirka wa Umar Buta harsashi, nan take kuwa ya rasu
” Bayan shi, an samu wani da harsashin amma bai mutu ba sai dai yana asibiti kwance a na duba shi.
” Tsakani da Allah yaya za muyi da ran mu a Kaduna, dukkan mu talakawa ne a haka ma da kyar muke iya biyan kuɗin makaranta. Yanzu da aka zuka mana kari, yaya zamu yi?, Shina ya sa muka fito don nunawa gwamnati rashin jin daɗin mu.
Wani shugaban matasa dake zaune a garin Jema’a ya shaida wa wakilin mu cewa, gwamnatin jihar ta hana yin zanga-zanga a yankin kudancin Kaduna, domin da zarar an fara zanga-zanga, yakan rikiɗe ne a ɓarke da rikicin addini da ƙabilanci.
” Ya kamata matasa su rika nuna fushin su ta wani hanyar ba fitowa zanga-zanga ba saboda haɗarin dake cikin sa.
A karshe Tahir ya roki gwamnatin jihar Kaduna ta sake duba wannan ƙari da tayi domin a rage wa ɗalibai.
Haka nan shima shugaban kwalejin ya tabbatar da kashe wannan ɗalibi da jami’an tsaro suka yi, kuma ya ce ba a makarantar ba ne ɗaliban suka yi zanga-zangar, sun tare babban titi ne.
Rundunar ƴan sandan Kaduna ta bayyana cewa masu zanga-zanga sun tare tawagar kwamandan sojoji a babban titin Da ya ratsa ta gaban wannan Kwaleji.
Ɗaliban suka tirje har sai da ya kai ga an ji wa shi kansa kwamandan da wani jami’in soja rauni. Su kuma a wajen kare janar ɗin aka ji wa wasu dalibai uku ciwo, ɗaya daga cikin su ya cika a asibiti.