Matasan PDP da suka garƙame malaman zaɓen hukumar Zaɓe na jihar Jigawa sun sake su bayan bayyana ɗan takarar PDP yayi nasara a zaɓen Kansila na wannan gunduma.
Matasa sun garƙame su a wasu ajujuwa tun ranar Asabar bayan malamin zaɓen da zai bayyana sakamakon zaɓe ya arce da takardun zaɓe saboda PDP ta yi nasara.
Daga karshe dai sai da gwamnan jihar Muhammadu Badaru ya umarci malamin zaɓen ya bayyana a maza-maza ya faɗi wanda ya ci zaɓen.
Daga baya jami’in ya bayyana ya kuma faɗi cewa ɗan takaran Kansila na PDP Yunusa Abdul ya yi nasara akan ɗan takaran APC Ja’afar Musa.
Yunusa ya samu kuri’u sama da 3000, shi ko Ja’afar na APC ya samu kuri’u 600 da ƴan kai.
Bayyana sakamakon ke da wuya sai aka barke da buki. Matasa suka rika kiɗa suna rawa suna murna ɗan takaran su yayi nasarar zama Kansilan gundumar Chiyako.
Matasa sun garƙame malaman zaɓe a Jigawa
Matasan PDP dake mazabar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a karamar hukumar Birnin Kudu sun bayyana cewa, bayan ƙirga ƙuri’un zaɓen da aka jefa kuma aka tabbatar PDP ce ta yi nasara sai, malamin zaɓen da zai bayyana sakamakon ya arce. Aka neme sa sama ko kasa ba a ganshi ba.
Wannan dalili ne ya sa matasa su ka fusata suka tattara sauran jami’an zaɓen suka kulle su a wasu ajujuwa suka ce sai malamin zaɓen da ya arce ya dawo ya bayyana sakamakon zaɓen tukunna za su buɗe su.
Matasan sun kawo wa jami’an zaɓen da suka garƙame abincin safe ranar Lahadi, bayan sun kwana a kulle, sannan suka mika musu ledoji ga duk wanda yake bukatar yin bahaya ko fitsari ya yi a ciki.
Kafin su garƙame wadannan jami’ai sai da suka ciccinnawa tayoyin motoci wuta a tituna suna zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaɓen.
Gwamna Badaru ya sa baki
Sai dai kuma a ranar Lahadi gwamnan jihar Badaru Mohammed ya fidda sanarwar lallai hukumar zaɓen jihar ta bayyana sakamakon za ben da akayi a fadin jihar.
Badaru ya kara da cewa, gwamnati ta gamsu da yadda aka gudanar da zabukan a fadin jihar.
” Ina kira ga jami’an hukumar zabe su gaggauta bayyana sakamakon zaben da aka yi. Gwamnati ta yi na’am da yadda aka gudanar da zaɓenncikin kwanciyar hankali ba tare da an samu hayaniya ba.
PDP ta yi korafin tsawwala kudin saida fom din takara, tana mai cewa gwamnati ta yi haka ne don ta hana ƴan PDP yin takara.
Discussion about this post