Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa kashe 30% bisa 100% na kuɗaɗen da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ke bayarwa a matsayin tallafi, duk cikin aljifai jami’an su da jami’an Ƙungiyoyin Sa-kai (INGOs) su ke tafiya.
Ya ce da yawan talakawa da al’ummar da su ka tarayya dalilin rikicin Boko Haram, duk ba su amfana da tallafin kuɗaɗen da manyan ƙungiyoyin ƙasashen duniya ke bayarwa da nufin ƙungiyoyin su samar da wasu kayan abinci da magunguna da makamantan su.
Gwamna Zulum ya yi wannan kakkausan furuci a cikin ɓacin rai ne ga Jakadiyar Amurka da Jakadiyar Birtaniya a Najeriya su ka kai masa ziyara a Maiduguri, babban birnin jihar.
“Za ku sanar da fitar maƙudan kuɗaɗe domin ayyukan tallafi da inganta rayuwar al’ummar da yaƙe-yaƙen Boko Haram ya kassara. Amma kashi 30% bisa 100% na waɗannan maƙudan kuɗaɗen duk aljihun jami’an UN ko na ƙungiyoyin ayyukan agajin sa-kai (NGOs) kuɗaɗen ke tafiya.
“Mu ɗin nan mu ke cikin jihar nan, mu muka san sashe da yankunan da ake da buƙatar tallafi ko wasu ayyukan jinƙai. Amma sai ku aiko da kuɗi, su yi mirsisi su je su danne na dannewa su yi aiki da sauran.
“Ban ga yadda za a yi a ce ayyukan jinƙai sun yi tasiri ba tare da an saka gwamnatin Jihar Barno a ciki ba. Saboda mu mu ka san inda abin ya fi shafa da waɗanda su ka fi shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
“Ayyukan UNDP ya na tasiri sosai ga rayuwar al’ummar da ake so a yi wa aikin, saboda sun saka gwamnatin jihar Barno a cikin aikin.
“Ba alfahari na ke ba. Tun ina Kwamishina na ke gudanarwa da aiwatar da ayyukan al’umma. Har yanzu ina Gwamna amma nisa sanar da ku ban taɓa karkatar da ko naira ɗaya ba.
“Mu ba kuɗin ku mu ke buƙata ko jira su zo mu danne ba. Abin da kawai mu ke buƙata shi ne wadanda ku ke damƙa wa kuɗaɗen su riƙa tuntuɓar mu ana yin aikin da za a yi da kuɗin tare da Gwamnatin Jihar Barno. Saboda mu mu ka san sirrin jihar mu ba su ba.”
Tun da farko sai da jakadun biyu, Mary Leonard ta Amurka da Catriana Laing ta Birtaniya su ka kai jiyara sansanonin ‘yan gudun hijira, sansanonin sojoji, ofishin ƙungiyoyin ayyukan jinƙai kafin su kai wa Gwamna Zulum ziyara.
Baban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon ne ya jagorance su wajen ziyarar da rangadin da su ka yi.
Su biyu tare da Kallon sun ƙara jaddada wa Zulum ci gaba da bayar da agajin duk da ya wajaba su riƙa bayarwa domin sauƙaƙa rayuwar waɗanda Boko Haram ya yi wa illa.
A na sa jawabin, Kallon ya ce Boko Haram sun kori mutum sama da miliyan 3.2 daga gidajen su. Sun rasa muhalli, wasu mutum miliyan 4.4 na fama da matsananciyar yunwa. Sannan kuma daga cikin mutane miliyan 13.1 da ke zaune a yankunan da Boko Haram su ka fi illatarwa, mutum miliyan 8.7 su na fama da bukatar cin yau da na gobe.
Discussion about this post