Hadin gwiwar jami’an tsaro a ranar Laraba sun fatattaki mahara da suka kai hari a wane rugar Fulani dake a wajen gari a karamar hukumar Anka a Jihar Zamfara.
Mai magana da yawun yan Sanda a Zamfara, Muhammed Shehu, ya shaidawa yan jaridu cewa jami’an tsaron sun kuma kwato Shanu masu tarin yawa da yan bindigar suka sace.
“Hadin gwiwar Jami’an tsaron wanda ya hada da sojiji da yan sanda sun bude wa yan bindiga wuta, suka tarwasasu cikin daji, da damansu sun tsira da raunuka, inji kakakin na yan Sanda.
“Dukkanin shanun da suka sace a rugar fulanin an kwatosu, jami’an tsaron suna cigaba da shawagi a yankin da abun ya faru domin kawar da barazanar kai wani sabon hari, inji kakakin na yan sanda.
Kwamishinan yan sandan jihar, Hussaini Rabiu, ya yabawa kokarin jami’an tsaron wajen fatattakan barayin ya kuma umarci su da cigaba da aiki wajen kawo zaman lafiya a jahir ta Zamfara mai fama da harin yan bindiga.
Kwamishinan yayi kira ga mutane dasu taimakawa jami’an tsaro wajen bada bayanai akan lokaci domin kawo karshin harin yan bindiga.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ranar Laraba, ya umarci ‘Yan sanda su bindige duk wani da aka gani rike da bindiga ko makamin da ba a amince da arika rike ta a fadin jihar.
Matawalle da kansa ya bayyana haka bayan ya kai ziyara ofishin ‘yan sandan jihar a Gusau.