Sakamakon damuwa kan matsalar tsaro, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za a fara aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR) a ranar 19 ga Yuli.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taro da ya yi da manema labarai tare da ƙaddamar da gidan yana na musamman don aikin rajistar masu zaɓen a ranar Alhamis a Abuja.
Yakubu ya ce a yayin da za a soma aikin rajistar ta hanyar yanar gizo a ranar 28 ga Yuni a duk faɗin ƙasar nan, za a fara aikin a sarari a ofisoshin hukumar na ƙananan hukumomi da na jihohi ne a ranar 19 ga Yuli.
Shugaban ya ce an yanke shawarar yin haka ne tare da tuntuɓar dukkan masu ruwa da tsaki saboda ganin yanayin rashin tsaro da ake ciki a ƙasar nan.
Ya tuno da cewa ko kwanan nan an kai wa ofisoshin hukumar hari a wasu sassan ƙasar nan, inda aka ƙone wasu, aka kuma ɓarnata wasu.
Yakubu ya ce a bayyane yake ƙarara cewa burin masu kai harin shi ne su yi zagon ƙasa ga ƙarfin da hukumar ke da shi na shirya zaɓuɓɓuka da sauran ayyukan da su ka danganci zaɓe, irin su aikin rajistar masu zaɓe.
Ya ce, “Mun ci sa’a, gine-gine da kayan aiki kaɗai aka ɓarnata. Duk da yake hare-haren sun ragu, har yanzu hukumar ta na matuƙar damuwa da barazanar da za su iya kawowa ga mutane masu zuwa yin rajista a lokacin aikin rajistar.
“A sakamakon wannan babbar damuwar, hukumar ta miƙa buƙatun ta ga gwamnati kuma ta yi zaman musamman da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin, ciki har da hukumomin tsaro a ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓa Tsakanin Hukumomi kan Tsaron Harkar Zaɓe, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES), da jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kan su da kuma kafafen yaɗa labarai.
“A lokacin waɗannan zaman mitin da mu ka yi, mun yi musayar tsare-tsare, burikan mu da damuwar mu dangane da irin barazanar rashin tsaro da mu ka fuskanta kwanan nan.
“Daga zaman da mu ka yi, masu ruwa da tsakin sun cimma matsaya cewa ya na da kyau wannan hukuma ta ɗauki batun tsaron rayukan masu zuwa rajista da kuma ma’aikata da matuƙar muhimmanci, sannan ta tsare tsadaddun kayan aikin da za a tura domin gudanar da aikin.
“Daga nan sun bada shawarar cewa ya kamata hukumar ta yi aiki da tsarin bi daki-daki a aikin rajistar masu zaɓen ta hanyar farawa a yanar gizo.
“Bayan an yi nazarin yanayin, to sai aikin ya ci gaba a sarari, wato ido na ganin ido, a ofisoshin hedikwarar jiha da na ƙananan hukumoni kafin a ƙarshe a fara a dukkan cibiyoyi guda 2,673 da ke faɗin ƙasar nan.
“Bisa ga wannan shawara, hukumar ta yanke shawarar bin tsarin fara aiki da dakatar da aiki ta yadda cibiyoyin rajistar za su kasance ana zuwa wajen su ba tare da wata matsala ba, sannan su na da tsaro.
“Bayan an duba waɗannan shawarwari a tsanake, sai hukumar ta yanke shawarar yin garambawul ga tsarin ta na gudanar da aikin, kamar haka:
“Za a fara gudanar da aikin rajistar kaɗai a ranar 28 ga Yuni, ta hanyar gidan yanar rajista na INEC, wato https://cvr.inecnigeria.org ko kuma https://cvr.inec.gov.ng
“Tsarin ba masu zaɓe lokutan yin rajista ta yanar gizo da ta sarari, a ofisoshin INEC na jiha da na ƙananan hukumomi zai fara a faɗin ƙasar nan a ranar 19 ga Yuli 19.
“Za a yanke shawara kan ranar da za a fara rajista a sarari a dukkan cibiyoyin yin rajista guda 2,673 da ke faɗin ƙasar nan bisa ga yadda aka ga yanayin tsaron.
“Ina so in yi kira ga ‘yan Nijeriya da su fahimce mu kuma su ba mu haɗin kai, musamman ma waɗanda su ke ta jiran ranar da za a ci gaba da wannan aiki na rajistar masu zaɓe.
“Wannan wani yanayi ne da ya fi ƙarfin hukumar zaɓe, idan an lura da ƙoƙarin da mu ke yi na tabbatar da cewa an yi dukkan ayyukan zaɓe a cikin lumana da kwanciyar rai.”
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa za a buɗe gidan yanar a wannin farko na ranar 28 ga Yuni.