Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ya bayyana cewa yana fatan ƴan Najeriya za su yi masa adalci idan za su tuna da shi bayan ya sauka a mulkin kasar nan.
Buhari ya faɗi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wakilin gidan talbijin din Arise ranar Alhamis.
Ya ce fatar sa shine a faɗi gaskiya, sannan yi masa adalci idan za a bada labarin abubuwan da ya yi na ci gaba a kasar nan bayan ya sauka.