Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya kalubalaci gwamnati Nasir El-Rufai cewa ayyukan gine-ginen titi da yake yi a Kaduna duk idan aka hada su ba kai Titin Yakowa guda daya tal ba wanda aka yi a jihar Kaduna ba, wanda kuma gwamnatin PDP ce ta yi.
A hira da tsohon gwamnan yayi da BBC Hausa, Yero ya kara da cewa ” Garin Kaduna ne kadai a jihar Kaduna ko garin Zaria ne kadai a jihar Kaduna. Mu gwamnatin mu na PDP mun yi la’akari da Kananan hukumomi 23 sune yan Jihar Kaduna kuma kowanne yana da hakki, kuma ko ina kaje a kananan hukumomin nan 23 PDP sun yi ayyuka daban-daban.
” Kuma ida ka hada duka titunan da ake yi da tsawon titin gaba daya ban jin ya kai titin Yakowa tsawo. kuma mu muna yin tituna ne ta yadda zai bunkasa mutane ba titunanan da zai zo ya bunkasa kasuwannin wasu ba.
” Ita gwamnati ba kamfani bane da take neman riba, gwamnati na yin abubuwan tane domin a kyautata wa mutane da kuma a samu zaman lafiya. Mu dauki gwamnati a matsain ta samu wa mutane ayyukan da zata yi ba don samun riba ba.
Ya ce duk da maganar samar da tsaro ne jam’iyyar APC ta yi kamfen akai, matsalar tsaro ya tabarbare a Kasar nan fiye da yadda jam’iyyar ta same shi a lokacin mulkin PDP.