Hukumar DSS basu kamani ba – Sheikh Gumi

0

Fitaccen Malamin addinin musulumcin nan kuma mazaunin Kaduna, Ahmad Gumi ya musanta labarin da ake yadawa cewa hukumar tsaro na sirri (DSS) sun kama shi bisa furuci da yake yi a akan ƴan bindiga.

Gumi yace yana nan daram a Kaduna babu wata hukuma data gayyace shi ko kamashi.

“Ina ta samun kiran wayoyi daga ko’ina a duniya ana tambayata cewa wai da gaske ne hukumar DSS ta kamani, amma gaskiyar magana ita ce babu wanda ya kama ni, sheikh Gumi ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Gumi, wanda tsohon Soja ne kuma mai sukar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, yana yawan kira a kafafen yada labarai cewa ayi wa Fulani makiyaya adalci kamar yadda ake yi wa sauran ƴan kasa wajen sama masu ababen more rayuwa.

A makon da ya gabata, Gumi yayi hira da gidan talbijin din (Arise TV) inda yake zargin wasu batagari cikin jami’an tsaro na hada kai da ƴan bindiga suna basu makamai, hakan ya jawo wasu ƴan Najeriya yin kira a Soshiyal Midiya cewa lallai aka ma shi,a bincike waɗannan kalamai da yayi.

“Ina da alaka mai kyau da jami’an tsaron Najeriya, kuma ban taba zuwa cikin daji wajen ƴan bindiga ni kaɗai ba, ba tare da jami’an tsaro da kuma wakilan gwamnatin Jaha da Fulani makiyaya da kuma masu wakilan al’umma ba.

“Kuma zan cigaba da tuntubar ƴan bindiga Kai tsaye ko ta hannun wakilai da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin samun zaman lafiya da arziki mai yalwa.

“Ina tabbatar wa mutane cewa babu wani sabani tsakani na da jami’an tsaro kuma zamu cigaba da hada kai har sai gaskiya ta tabbata a Najeriya da izinin Allah”.

Share.

game da Author