HUDUBAR SABON SUFETO JANAR: Kada ƴan sanda su sake barin ƴan iska su banka wa ofisoshin su wuta

0

Sufeto Janar na ƴan Sandan Najeriya ya hori daukacin ‘yan sanda su sani cewa a yanzu an dauko hanyoyin samar masu da ababen more rayuka da kulawa fiye da gwamnatocin baya.

Usman Baba ya roki ‘yan sanda su daina kashe kan su da kan su, domin za a ci gaba da na su kulawa fiye da baya.

Da ya ke magana yayin da ya kai ziyara Jihar Lagos, ya hore su da su kara mikewa tsaye kyam su tsaya wajen kare dukiyoyi da rayukan jama’a da kuma nasu na su rayukan.

Usman dai sai da ya fara biyawa Gidan Gwamnatin Jihar Lagos, inda ya fara ganawa da Gwamna Babajide Sanyo-Olu kafin tukunna ya zarce Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Jihar Lagos.

Yayin da ya ke wa jami’ai jawabi ana tsakiyar sheka ruwan sama, ya ce “ana kan karin kulawa da lafiya da rayukan ku. Don haka kada ku rika kashe kan ku da kan ku.”

Ya hore su wajen kara zage damtse wajen kare kadarorin jama’a da.

“Daga yau kada na kara jin wasu ‘yan iska sun banka wa ofisoshin ku wuta don kawai sun rike bindiga, sanduna da adduna.”

A karshe ya hore su cewa su rika yi wa bindigogin su linzami, “saboda akwai lokacin amfani da bindiga da kuma dalilan yin amfani da ita.”

Share.

game da Author