HIMMA DAI MATA MANOMA: Aisha, lauyar da ta ajiye aikin lauya, ta lauye zuwa harkar noma

0

Aishat Titilola ba tsohuwa ba ce, shekarun ta 29, amma ita ce ke da katafariyar gonar kiwon dabbobi mai suna TAD Farms a Jihar Oyo.

Aisha lauya ce, wadda ta yi digiri na ɗaya a fannin lauya a Jami’ar Bedfordshire, a garin Luton na ƙasar Ingila. Sannan kuma ta na da wata ƙungiya mai suna African Child Liberation Mission.

Aisha ta ajiye aikin lauya gefe ɗaya, ta lauye ta bada himma wajen kiwon awaki, tumaki da zomaye. A yanzu a harkar kiwo Aisha ta yi ƙarfin da har ma’aikata 11 ke aiki a ƙarƙashin kulawar ta. Cikin su akwai mata tara, maza uku.

Tun Ina NYSC Na Fara Kasuwancin Awakai Da Tumakai

“Bayan kammala digiri na cikin 2014, kuma ta zarce kwas na dole, to da na tafi NYSC cikin 2016 sai na fara sayar da awakai da tumakai.

“Idan lokacin shagulgulan Sallah ko Kirsimeti ya yi, sai na tafi Arewa na sayo awakai da tumakai na kawo Kudu na sayar. To daga nan sai na zarce kiwo kawai, kuma na riƙa haɗawa da noman zamani.”

Da wakilin mu ya tambaye ta dalilin ajiye aikin lauyan da ta shafe shekaru shida ta na yi, inda har Ingila ta je ta yi digiri, sai Aishat ta ce: “A gaskiya ni mace ce mai kazar-kazar. To da na fara aikin lauya ɗin, sai na fahimce ba harka ba ce ba ce mai sa kazar-kazar da jiki. Ganin haka sai na ce tunda dama ni tun ina ƙanƙanuwa na ke sha’awar noma da kiwo, gara kawai na mallaki gona na shiga harkar noma da kiwo gadan-gadan.

“Yadda na samu ‘yan kuɗin da na fara kiwo da noma gadan-gadan da su kuwa, bayan na gama digiri a Ingila, sai na tsaya can na ɗan yi aikin da na tara ‘yan kuɗi kafin na dawo gida.

“To ganin yadda na fara abin da himma, sai iyaye na da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki su ka riƙa tallafa min da kuɗi. Daga nan kuma sai masu sha’awar zuba jari su ka antayo kuɗaɗen su a harkar. Domin ba don su ba, da harkar ta kakare. Saboda sai da ɗan jarin nawa ya lume gaba ɗaya cikin harkar.

“Amma ka ga a yanzu ba a rasa dabbibi 200 a wurin mu, waɗanda kuma duk na kiwo ne. Idan su ka haihu sai mu kiwata ‘ya’yan, su girma mu sayar. Kuma mu na sayo wasu dabbobin kai-tsaye daga wasu masu kiwon, sai mu yanka mu sayar ga masu harkaf nama.”

Ƙulubalen Da Na Ke Fuskanta A Harkar Noma Da Kiwo

“Ka ga na farko akwai tsare-tsaren gwamnati wadanda ba su da kan-gado ballantana alfanu. Akwai matsala ta rashin kyan hanyoyi, sannan kuma za ka ji a kullum gwamnati na cewa ta na bayar da tallafin noma. Amma mu manoman na gaskiya ba samun wannan kuɗaɗen tallafin mu ke yi ba.

“Sannan ga babbar matsalar rashin wuta. Gaba daya daga safiya har wata safiyar da janareta na ke aiki. To ka ga kuwa sana’a irin haka ba za ka iya goyayya da masu irin sana’ar ka na wasu ƙaashen ba.”

Sannan ga wata gagarimar matsala, ta rashin tsaro. Mutane da yawa sun ƙaurace wa harkokin noma a gonaki, saboda su na gudun masu garkuwa da mutane. Daga gida zuwa gona ta, tafiyar awa 1:45 ce. Kuma ana sace mutane a yi garkuwa da su a hanyar. A shekarun baya a kullum na ke zuwa gona. Amma yanzu ba kowace rana na ke zuwa ba. To kuma fashin da na ke yi ya kan haifar da cikas a harkar inganta noman da kiwon.”

Aishat ta shaida wa wakilin mu cewa ba ta sha walaha samun goma mai faɗin hekta hudu da ta ke kiwo a ciki ba.

” Batun yadda na ke ciyar da dabbobin kuwa, ina ciyar da su ne da bawon rogo, sai kuma ciyawar da na ke nomawa wacce ake fara diba ana ciyar da dabbibin cikin makonni uku bayan shuka ta.”

Share.

game da Author