Hajji 2021: Hana baki zuwa Hajjin bana yin Allah – Shugaban NAHCON

0

Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa Zikirullah Hassan ya bayyana cewa rashin zuwa aikin Hajji da mutane ba za su yi, yin Allah ne ba mutum ba.

” Tun kafin a yi duniya haka Allah ya tsara, bana ma ba ki ba zasu aikin hajji ba, mun amshi wannan sako na da kyakkyawar fahimta, fatan mu shine Allah ya kawo karshen wannan jarabawa, Amin.

Idan ba a manta ba Kasar Saudiyya ta bayyana cewa babu wani maniyyaci da zai je aikin Hajjin 2021 na bana, saboda kauce wa yaɗuwar cutar korona.

Sanarwar dai na nufin babu maniyyaci ko ɗaya da za a bari ya shiga daga Najeriya da sauran ƙasashe.

Jaridar Arab News, Saudi Gazzete da wasu jaridun Najeriya sun ruwaito cewa mahukuntan ƙasar sun ce mutum 60,000 ɗin da a watan jiya aka amince za su yi aikin Hajjin 2021, za su kasance duk ‘yan ƙasar Saudiyya ne, sai kuma ‘yan sauran ƙasashe da ke zaune a cikin ƙasar Saudiyya ɗin.

Wannan hukunci da Saudiyya ta kafa, ya shafe sanarwar farko wadda ƙasar ta gindaya sharuɗɗan da maniyyaci daga ƙasashen waje za su cika kafin su shiga ƙasar Saudiyya aikin Hajjin bana.

Za a fara aikin Hajji a tsakiyar watan Yuli, inda a karo na biyu ma aka hana ƙasashen waje halarta, bayan hana su da aka yi a 2020.

Tsohuwar Dokar Shiga Saudiyya Aikin Hajji, Kafin Hana Kasashe Shiga:

Kasar Saudiyya ta gindiya sharudda guda 10 tsaurara wajen gudanar da ayyukan Hajjin bana na 2021.

Daga cikin sharuddan dai an hana dattawa masu shekaru 61 zuwa sama zuwa aikin Hajji, kuma an hana kananan yaran da ba su kai shekaru 18 a duniya ba.

Saudiyya ta kuma ce gaba daya mutum 60,000 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana. Kuma za su kasance a cikin su din ma akwai ‘yan kasar Saudiyya.

Kafin bullar korona dai akan samu mahajjata har miliyan 2.5 ko sama da haka a lokaci guda.

Share.

game da Author