Gwamna Balan Bauchi ya naɗa Aminu Gamawa sabon shugaban ma’aikata fadar gwamnatin jihar

0

Bayan cire tsohon shugaban gidan Radiyon Tarayya, Ladan Salihu a matsayin shugaban fadar gwamnatin jihar Bauchi da gwamnan jihar Bala Mohammed yayi a makon jiya, gwamnan ya naɗa Aminu Gamawa sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Idan ba a manta ba, gwamna Bala ya cire kafatanin kwamishinonin sa tare da sakataren gwamnatin jihar har da shugaban fadar gwamnatin jihar Ladan Salihu a wani garambawul da yayi wa yan siyasa da aka nada makamai a jihar.

An naɗa Gamawa kwamishinan Harkokin Kudi da tsare-tsare na jihar Bauchi a 2019, kuma shine shugaban kwamitin Korona na jihar.

Wannan naɗi zai fara aiki ne nan take.

Share.

game da Author