Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru, don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa. Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.
Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa. Wata tawagar alƙalai waɗanda ba ma’aikatan BBC ba ne, da ta ƙunshi malaman jami’a za su zaɓi gwarzuwa ɗaya da labarinta ya yi nasarar yin na ɗaya sannan za su zaɓi ta biyu da ta uku. Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa za a cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba za a aika masu ko wane irin bayani kan masu shiga gasar ba.
Waɗanda su ka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi $2,000 ga wadda ta zo ta ɗaya, $1,000 ga wadda ta zo ta biyu, $500 ga wadda ta zo ta uku.
BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa. Duka labaran da aka naɗa za su ƙunshi sunan labarin da sunan marubuciyar. Ma’aikatan BBC Hausa za su karanta labaran da suka cancanci yabo cikin mako 12. Waɗanda suka yi nasara za su karanta labarinsu gaba ɗaya da kansu a ɗakin gabatar da shirye-shirye na BBC.
An buɗe shiga gasar da ƙarfe 10.00 agogon GMT, wato karfe 11.00 agogon Najeriya da Nijar ranar 31 ga watan Mayun 2021.
Za a rufe karɓar labarai ranar 16 ga watan Agusta 2021 da ƙarfe 11.59 agogon GMT. Duk wacce ta aiko da labarinta bayan nan ba za a karɓa ba.
A shekarar bara, Maryam Umar, daliba a jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto ta zo na daya da labarin ta mai suna ” Rai Da Cuta”.
Ku bi nan don samun cikakken bayani
Discussion about this post