Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa garkuwa da daliban makaranta da aka yi a jihar Kebbi ya tabbatar da tsananin rashin tsaron da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
El-Rufa’i ya fadi haka ne da yake jawabi a fadar gwamnatin jihar Kebbi lokacin ziyarar jaje da ya kai wa gwamnan jihar Atiku Bagudu ranar Alhamis.
“A baya kafin aukuwar wannan al’amari, ana murna cewa ita jihar Kebbi ba ta fama da matsalolin rashin tsaro kamar yadda jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da Kaduna ke fama da shi.”
El-Rufa’i ya ce rashin tsaron da jihar Kebbi ke fama da shi zai iya kawo cikas wajen noman abinci a jihar.
“Sanin kowa ne cewa jihar Kebbi ta yi suna wajen noman shinkafa wanda shinkafa yanzu ya zama abincin kowa da kowa a kasar nan. A dalilin haka hankalin mu dole ya tashi saboda idan matsalar rashin tsaro ya afkawa jihar za a samu matsalar larancin abinci.
El-Rufa’i ya jinjina kokarin da gwamnatin tarayya da duk jami’an tsaro ke yi wajen samar da tsaro a kasar nan.
Ya ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Da yake nasa jawabin gwamnan jihar Atiku Bagudu ya godewa gwamna El-Rufa’i na ziyarar jaje da ya kawo wa jihar da addu’o’i da suka rika yi wa jihar kan abinda ya afka musu.
Bagudu ya ce garkuwa da daliban makarantar da aka yi na neman dawo da hannun agogo baya na ci gaba da ake samu, ba jihar Kebbi ba kawai, har da kasa baki daya.
Yayi kira da a maida hankali wajen ganin an tunkari wannan matsala ba tare da ana fargaba ko tsoro ba.