Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bada umurnin yin kidayar Fulani makiyaya ƴan asalin jihar da wadanda suka fita kiwo a faɗin kasar nan.
Ganduje ya faɗi haka ne a taron da ya yi da gidajen jaridu dake jihar a cikin wannan mako.
Ya ce gwamnati za ta yi haka ne domin sanin alkaluman Fulani makiyaya dake zaune a jihar suna kiwo da wadanda ƴan asalin jihar ne amma suna wajen jihar kiwo. Sannan kuma ya kara da cewa gwamnati za ta gina rugagen f Fulani a dajin Dansoshiya.
Ya ce gwamnati ta fara tattaunawa da kwararru kan yadda za a shuka ciyawar da za a ciyar da dabbobin sannan da gina ababen more rayuwa domin walwalan makiyayan da za su zauna a rugan.
Rikicin Fulani makiyaya da manoma matsala ce da ya dade yana aukuwa a kasar nan.
Zuwa yanzu dai wasu jihohi a kasar nan sun kafa dokar hana kiwon dabbobi a fili.
Idan ba manta ba Ganduje ya taba cewa gwamnatinsa za ta mayar da wasu dazuka biyar a jihar rugagen Fulani.
Ya ce gwamnati za ta gina makarantu, asibiti, kasuwa da ofishin ‘yan sanda domin ganin Fulanin da za su zauna sun samu walwala a rugagensu.
Ganduje ya ce gina rugage hidimace na gwamnatocin jihohi ba na gwamnatin tarayya ba domin sune suka fi mu’amula da makiyayan