Ganduje ya janye karar da ya shigar na ƙalubalantar bidiyon da J’aafar ya wallafa ya na cusa daloli a aljihun sa

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya janye karar da ya shigar yana ƙalubalantar bidiyon da mawallafin jaridar Daily Nigeran Ja’afar Ja’afar ya wallafa wanda ke nuna shi ya na zura daloli a aljifan jamfar sa.

Idan ba a manta a wata hira da Ganduje yayi da BBC ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba gaskiya za ta bayyana kuma zai karyata jaridar Daily Nigerian.

Sai dai kuma kafin akai ga yin fallasan, sai Ja’afar ya yi zargin ana bibiyan rayusar sa dana iyalan sa.

Daga nan sai ya tattara nasa Ina sa ya kwashe ilansa kaf ya nausa da su kasar Birtaniya, tsoran kada wani abin bazata ya afka masa da iyalan sa.

Sai dai kuma kakkwarar majiya ta shaida mana cewa gwamna Ganduje na shirin shigar da sabuwar kara akan Ja’afar ne ganin wasu da ke masu shaida ne dake tare da Ganduje basu tare .

Salihu Tanko wanda hadimin sa kuma mainbada shaida a shari’ar, ba ya tare da gwamna Ganduje.

Waɗannan sune ake ganin na daga cikin ɗalilan da ya sa Ganduje ya janye karar zai kuma sake aikawa da ita a fasali da ban.

Idan ba a manta ba Ganduje ya tsige Tanko bayan ya bayan ya yi wasu kalamai kan shugaban kasa Muhammadu Buhari da bai yi wa gwamna daɗi.

Share.

game da Author