GADANGARƘAMA: Ban aika wa Buhari gurguwar shawarar jingine Kundin Tsarin Mulki ya kafa Dokar-ta-baci ba – Malami

0

Ministan Harkokin Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya ƙaryata rahoton da wata jarida mai suna ‘Gazette’ ta buga cewa ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari wata shimfiɗeɗiyar wasiƙa inda ya shawarce shi ya jingine Kundin Dokokin Najeriya na 1999, ya kafa dokar-ta-bace domin ya shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

Jaridar ta wallafa a shafin ta na yanar gizo cewa, wannan shawara da Malami ya bayar ta na nufin a jingine dokar ɗungurugum, musamman Sashe Na Huɗu na Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda ya bai wa kowane ɗan Najeriya ‘yanci.

Kenan rahoton ya zargi Malami da bai wa Buhari shawarar a ɗage dokar a hana kowa ‘yanci, a yi amfani da gadangarƙamar dokar da za a yi amfani da jami’an tsaro a cimma manufar tirsasa jama’a tare da hana su kuka, ƙorafi ko kuma fitowa yin bore.

An ce Malami ya bada wannan shawara ce domin a ganin sa, ta wannan hanyar ɗage doka a kafa dokar-ta-baci, wadda a zamanin yaƙi ake kira ‘Marshal Law’ ce kaɗai za a iya daƙile matsalar tsaro a Najeriya.

An wallafa cewa Malami ya nuna wa Buhari cewa: “Sai an ɗage dokar tsarin mulkin Najeriya, domin hakan zai kawar da bata lokaci da jan-ƙafa da cike-cike da zaman tattaunawa neman mafita kafin a aiwatar da wani uzirin gaggawa, wanda ya danganci harkar tsaro a ƙasar nan.”

Ƙarya Da Sharri Makirai Su Ka Yi Min -Malami:

Sai dai kuma yayjn da Minista Malami ke maida raddi ta baki da hannun Kakakin Yaɗa Labaran sa, Umar Gwamdu, ya ce ƙarya ce kuma ƙirƙira ce aka shirya aka ce shi ya yi.

Gwandu a cikin wata wasiƙa da ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya ce babu yadda za a yi Minista Malami ya yi wannan bahagon tunanin bada shawarar a jingjne kundin dokokin tsarin mulki na 1999.

Ya ƙara da cewa Malami mutum ne mai kishin dimokradiyya da dukkan rassan inuwar dimokraɗiyyar baki ɗaya.

Share.

game da Author