GA LATTI GA FIRGITA: Yadda jirgin ƙasa ya lalace mana tsakiyar dokar daji tsakanin Abuja da Kaduna, Daga Abubakar Mohammed

0

Jama’a, Allah ya raba mu da wahala. Ku ce amin. Ni dai na tashi daga gida na a Kaduna a yau Litinin da nufin idan na yi asubanci zuwa tashar jirgin ƙasa ta Rigasa, to zai iya isa ofis aƙalla ƙarfe 10 na safe.

Na samu jirgin farko mu ka tashi da sassafe. Amma abin takaici kuma abin firgita da tashin hankali, mun shiga tsakiyar dokar daji inda babu gida, sai jirgin nan ya kakare. Tun mu na tunanin wata ‘yar ƙaramar matsala ce, har dai kowa ga gano cewa matsalar ba ƙarama ba ce. A nan fa kowa ido ya raina fata.

Wutar jirgi ta ɗauke. AC ta daina yi, tilas aka buɗe dukkan tagogi na kowane tarago, saboda kowa ya fara gumi.

Hatta lasifika ma dainawa ta yi, sai dai wani ma’aikaci ya riƙa bi tarago-tarago a guje ya na sanarwa.

Bayan mun ɗauki tsawon lokaci, sai aka sanar da mu cewa jirgin mu ba zai iya tafiya zuwa Abuja ba, sai dai a kawo wani kan jirgi a jona a taragon da mu ke ciki, sannan a kai mu gida. Hakan ma aka ce sai nan da awa biyu da rabi kan jirgin zai karaso a inda mu ke.

Nan fa duk aka fito aka yi zaune a kan titin jirgi birjik. Daga masu ƙorafi sai masu surfa zagi. Duk wanda ka gani a tsorace ya ke, saboda tunanin kada ‘yan bindiga su kewaye mu su tarkaɗa mu zuwa cikin daji.

Da ya ke daga inda jirgin ya kakare ana hangen kwalta, wasu fasinjoji sai su ka riƙa ɗaukar kayan su, su ka nufi bakin kwalta su na tsare motoci domin a kai su Abuja.

Mu na nan zaune a tsorace sai ga jirgin Kaduna wanda ya taso daga Abuja ya zo ya tsaya. Sai fasinjoji da dama su ka riƙa afkawa cikin sa, domin a koma da su Kaduna, daga can kuma su sake sayen tikiti jirgin ya koma da su Abuja.

Ashe sageheduwa su ka yi. Yayin da jirgin da ya kai fasinjoji Kaduna ya sauke, sai aka kwance kan jirgin, aka baro taragan jirgin, ya zo wurin na mu jirgin, aka ɗaura masa taragan da mu ke ciki.

Shi kan sa jirgin da ya dauket mu ɗin daga baya, an ce da ya baro Abuja, sai da ya kakare kan hanya.

Haka na isa ofis bayan ƙarfe ɗaya na rana. Sai dai kuma zan iya cewa tafiya ta yi albarka, domin Allah ya hana mu yaɗuwa da ‘yan bindiga. Ba mu hange su ba, ba su hango mu ba.

Share.

game da Author