An bayyana cewa a cikin shekarar 2019, Najeriya ta yi cinikin fetur da iskar gas har na dala biliyan 34.22.
Bayanin wanda ya fito daga NEITI, an kuma bayyana ƙididdigar cinikin fetur da gas wanda Najeriya ta samu cikin shekaru 10, daga 2010 zuwa 2019 ya kai dala biliyan 418.544.
NEITI ta bayyana cewa cinikin fetur da gas na 2019 ya haura na 2018 da dala biliyan 4.88.
Sannan kuma dalla-dallar lissafin ya nuna cewa a cikin 2019 ɗin, kamfanoni sun biya Gwamnatin Tarayya dala biliyan 18.90, na kuɗaɗen hada-hadar da ta shafi man fetur da gas.
Sai kuma cinikin da hukumomin da su ka jiɓinci harkokin mai da gas na gwamnati su ka tara dala biliyan 15.12 cikin 2019 ɗin dai.
A shekarar 2011 ce aka fi samun kuɗaɗen fetur har dala biliyan 66. 442.
Amma kuma a shekarar 2016 ce aka fi tara mafi ƙarancin kuɗi dala biliyan 17.055.
Sai dai duk da waɗannan maƙudan kuɗaɗen da Najeriya ke tarawa, bai sa ƙasar ta yi bunƙasar a zo a gani ba, bai hana ta yawan ciwo basussikan da su ka cika mata ciki ba.