Babban jojin kotu a jihar Cross River Akon Ikpeme ta yanke wa wani matashi mai suna Godswill Brownson mai shekaru 25 hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara 12 bayan ta kama shi da laifin yi wa yara kanana fyade.
Tun a watan Nuwamban 2017 ne aka Kai Brownson koto baya mahaifiyar yaran ta kama shi da yana aikata wannan ta’asa.
Alkalin kotun Akon ta yanke wannan hukunci ne bisa ga hujojjin da suka tabbatar cewa Brownson ya rika lalata da wadannan yara.
Lauyan da ya shigar da karan James Ibor ya ce Brownson ya dade yana yin lalata da wadannan yara wanda shekarunsu bai wuci bakwai da biyar ba.
“Mahaifiyar yan matan na zama a gidan kakan yaran wanda shi Brownson yake makwabcinsu.
“Brownson ya yi amfani da zaman mutuncin da ke tsakanin sa da iyayen yaran yana lalata da su.
Yi wa yara kananan fyade matsala ce dake yi wa kowace al’umma illa.
Wasu manazarta sun zakulo wasu hanyoyi da suke ganin za su yi tasiri matuka wajen rage aukuwar yawa-yawan fyade da ake yi wa yara kanana har da manya.
1. A hana ko a rage yawan aikawa da yara hutu gidajen ‘yan uwa, kakanni da abokan arziki ba tare da an tanadi kyakkyawar hanya da za a rika kula da saka musu ido ba. Domin bincike ya nuna makusantar yaran ne suka fi aikata haka akan yaran harda manya ma.
Mafiyawan lokuta ‘yan uwan iyayen yaran Wanda aka fi amincewa da su ne ke aikata irin wannan abu alokacin da suka faki babu wani babba a kusa da su.
Idan ya kama dole a je hutu uwa ta tabbatar ta tafi hutun tare da ‘ya’yan ta domin ta rika saka musu Ido a koda yaushe sannan tana kula da zirga-zirgar su.
2. A daina daukan mai raino, yarinyar zama da masu aiki ba tare da an tantance su sannan ana sa musu ido, ana bibiyar mu’amularsu da yaran gida.
Idan mace baza ta iya yin aikin cikin gidanta ba za ta iya daukar hadima na jeka-ka-dawo, wanda za ta zo ta yi aiki ta tafi.
3. Tarbiya
Rashin baiwa ‘ya’ya tarbiyya na gari na daga cikin abubuwan da ke bata su tun suna kanana. Sai kaga iyaye sun bar yaro tun yana karami yana kalle-kallen da bai kamata ba, wasu iyayen hatta fina-finan batsa suke kallo tare da ‘ya’yan su, wasu ma har saduwa da juna sukan yi a daki daya da ‘ya’yan su.
Sannan kuma da ba yaro tun yana karami damar yin abinda ya ga dama, a barshi kullum a jikin wannan namijin, wai kawon sa ne, wancan namijin wai baffan sa ne.
4 – Sa yaro a hanyar sanin Allah da tsoron sa da kuma nuna masa cewa ga irin abubuwan da zai rika yi idan baki suka zo ko kuma suka je unguwa. Kuma da zaran bai gamsu ba da wani abu da wani ya yi masa ya gayawa iyayen sa.