Kungiyar masu yin buredi dake baban birnin tarayya Abuja AMBCN ta bayyana cewa akwai yiwuwar farashin buredi zaitashi da kashi 30% a Abuja.
Shugaban kungiyar Ishaq Abdulkareem ya sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litini.
Abdulkareem ya ce farashin buredi zai tashi muddun ba a samu raguwar hauhawar farashin kudin Fulawa da Siga ba.
Shugaban kafanin Bon Bread Maria Cardillo ta koka da tsadar fulawa da siga da sauran sinadaran da ake amfani da su wajen hada buredi.
“A kan karin Naira 500 na farashin kayan hada buredi da muke siya dole zai shafi farashin buredi a kasuwa.
Discussion about this post