FALLASA: Yadda mai Tiwita ya dauki nauyin kudaden shirya zanga-zangar #EndSARS -Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa kamfanin Tiwita ya yi ladab, ya nemi zaman sulhuntawa da sasantawa da Gwamnatin Najeriya.

Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa halin da ake ciki tun bayan dakatar da Tiwita daga Najeriya.

Lai ya yi karin hasken ne bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Buhari a ranar Laraba.

Ministan ya kara jaddada cewa an karya fukafikin ‘yar tsuntsuwar Tiwita a Najeriya, saboda sun bayar da kofa ga wasu marasa kishin kasa su na amfani da kafar da nufin wargaza Najeriya.

Lai ya ce Shugaban Tiwita ne ya rika daukar nauyin dukkan kudaden da masu shirya tarzomar #EndSARS su ka kashe a lokacin zanga-zangar.

“Sannan kuma Tiwita ta bai wa Shugaban IPOB damar watsa sanarwar mambobin IPOB su rika kashe jami’an tsaro, kuma su rika banka wa kadarorin gwamnati wuta.”

Lai ya ce duk da Gwamnatin Najeriya ta yi ta rokon Tiwita cewa ta cire sanarwar Nnamdi Kanu da ya yi shelar a fara kisan ‘yan sanda ana banka wa kadarorin gwamnati wuta, Tiwita ta yi kunnen-uwar-shegu da kiraye-kirayen.

Daga ya lissafa sharuddan da ya ce tilas sai Tiwita ta cika kuma ta amince da su, kafin a amince ta ci gaba da aiki a Najeriya.

Share.

game da Author