Facebook zai dakatar da amfani da kafar a soshiyal midiya kyauta daga 2023

0

Daga 2023 ba za a iya yin mu’amula kai tsaye da shafin Facebook kyauta ba sai mutum ya biya dan wani kudi da Facebook zai saka domin amfani da kafar.

Shugaban Facebook Mark Zuckerberg, ya ce za a yi haka domin masu kirkiro bayanai su rika samun ribar abin da suke sakawa a shafin maimakon yadda yake kyauta yanzu.

Sannan ya kara da tabbatar da cewa ribar da Facebook zai rika samu yana rabawa da masu kirkirowa da saka bayanai zai riɓanya kudin da suke samu a wasu shafukan soshiyal midiya kamar Apple da sauransu.

” A yanzu dai kowa zai ci gaba da morar shafin mu kyauta har zuwa 2023, daga nan kuma za mu saka kudi ta yadda masu kirkiro bayanai da sakawa za su rika samun ribar abinda suke saka wa daga gare mu, sannan mu kuma za mu rika cajin kudi daga masu saka wa da karatu, ana raba ribar.

Sai dai kuma idan har Facebook ta yi nasarar aiwatar da wannan abu sjafin zai samu karin yawan mabiya wato masu amfani da shafin sannan kuma zai ba wasu shafukan dake yanar gizo yin irin haka domin samun ɗimbin riba, kuma masu mua’amula a shafin su amfani da samun kuɗin shiga.

Share.

game da Author