Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa da ga yanzu shafukan sada zumunta a yanar gizo, Tiwita, Facebook da sauran su sai sun yi rajista a Najeriya.
Bayan haka Lai Mohammed ya kara da cewa kamfanin Tiwita na neman ayi sulhu da Najeriya.
” Tiwita ta aiko da sakon tayi ga Najeriya, ta na so ayi sulhu kan dakatar da kamfanin da gwamnatin Najeriya domin a sasanta
Lai Mohammed ya ce Tiwita ta yi rashin kunya matuka sannan kuma saboda rainin wayau ta fito tana ruruta wutan ayi adawa da gwamnati cewa wai sakon Shugaba Buhari yayi karya dokar su.
” Sakon Buhari ne ya karya dokar Tiwita, ba ire-iren sakonninnda Nnamdi Kanu ya ke saka wa ba na ingiza mutanen sa su yi wa kasa bore ba. Sannan kuma a idon mu Tiwita ya rika marawa masu zanga-zangar EndSars baya har da kuɗaɗe.
Trump ya jinjina wa Buhari kan ‘rufe wa dan tsuntsun Tiwita baki’
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna yabo da jinjina ga Gwamnatin Najeriya saboda dakatar da amfani da Tiwita a Najeriya. Ya kuma yi kira ga sauran kasashe bi bayan Najeriya su kori Tiwita daga kasashen su.
“Ina taya Najeriya murna bisa kulle Tiwita saboda ta kulle shafin Shugaban kasar. Ya kamata wasu kasashe ma su yi rige-rigen kulle Tiwita da Facebook, saboda ba su bari jama’a na bayyana ‘yancin ra’ayin su.
“Nan ba da dadewa ba wasu masu irin kafar yada labarai irin na su duk za su fito su yi wa Tiwita da irin su kishiya.
“Ko da ni ne a kan mulki haka zan yi, amma sai Zuckerberg ya rika damu na da kira, kuma ya rika rika zuwa Fadar Shugaban Kasa ya na kwasar girkin hadadde, tare da yi min dadin baki ya na kambama ni.
Trump ya yi wadannan bayanan lokacin da aka dakatar da shi yin amfani da soshiyal midiya tsawon ahekaru biyu a Facebook.
Discussion about this post