Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya nada Madakin Lere, Suleiman Umaru sabon sarkin Lere.
Idan ba a manta ba tun bayan rasuwar sarki Abubakar II a watan Afirilu, ƴaƴan sarakunan masarautar Lere suka fantsama neman sarautar wannan masarauta.
Gwamna El-Rufai ya sanar da naɗin Madaki Suleiman, a matsayin sabon sarkin Lere ranar Juma’a.
Mai baiwa gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin yaɗa labarai Muyiwa Adekeye ya sanar da naɗin a wata sanarwa da ya saka wa hannu ranar Juma’a.
Tuni dai har buki ya barke a garin Lere inda ƴan uwa da abokan arziki suka rika yin turuwa zuwa fadan sabin sarki domin taya shi murna.
” Wannan naɗi ya farantawa mutanen Lere rai matuƙa, domin abinda kowa yayi fata a kai kenan. Madaki Suleiman mutum ne mai sanin ya kamata da kaunar zumunci. Yana da son jama’a da kuma kishin garin Lere. Muna taya shi murna da fatan Allah ya sanya albarka a cikin wannan sabon kujera da zai hau.” Kamar yadda Hassan Mohammed, ya sahida wa PREMIUM TIMES HAUSA.