El-Rufai da Akeredolu sun ci gaba da mu’amula da Tiwita duk da dokar gwamnati na kowa ya kaurace wa shafin

0

Gwamnonin Kaduna da Ondo, Nasir El-Rufai da Rotimi Akeredolu, sun ci gab da amfani da shafin Tiwiti kamar yadda ya nuna a wani sakonni da dukkan su biyu suka saka a shafukan.

A ranar lahadi an ga wani sako da gwamnan El-Rufai na Kaduna ya saka a shafin sa ta tiwiti, wani rubutu wanda wani dan jarida mai suna Nebojsa Malic, ya wallafa.

Shi ko gwamna Akeredolu na Ondo ya rubuta sakon rashin jindadin kisar da aka yi ne a garin Igangan, jihar Oyo.

Sai dai kuma wani jami’in gwamnatin Kaduna ya shaida cewa El-Rufai ba ya Najeriya, wanda a dalilin haka yasa yana da ikon yin amfani da tiwiti tunda dokar bata kai can kasar da yake ba.

Shi ko kakakin gwamna Akeredolu, Olabode Richard cewa yayi kawai sun ga tiwita ya bude ne a Najeriya, sai suka yi amfani da wannan dama suka saka sakonni.

Idan ba’a manta ba ministan shari’a, Abubakar Malami ya gargadi yan Najeriya su kaurace wa shafin Tiwita din, idan kuma mutum yaki zai ji a jikin sa.

Wannan gargadi ya gamu da suka daga ‘yan Najeriya inda suka cewa babu dokar da ta ba gwamnati damar hukunta mutum kawai don yay ci gaba da mu’amula da tiwita.

Haka kuma har zuwa litinin din yau, gwamnati na ci gaba da fitta sakonni game da dakatar da shafin tiwita din a Najeriya.

Share.

game da Author