DUNIYA MASAKIN KUNU: Yadda ƙasashen Spain Da Portugal Su Ka Kasance Ƙarƙashin Daular Musulunci tsakanin 711-1491

0

Sunayen garuruwan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar da mu ke gani na ƙasar Spain, irin su Zaragoza, Seville, Almeria, Barcelona, Madrid, Murcia, Albacete, Cardiz, Granada, Cordova, Valencia Malaga, kai har da Lisbon, babban birnin ƙasar Portugal, duk sun taba kasancewa a ƙarƙashin Sarakunan Daular Musulunci tsawon ɗaruruwan shekaru. Ku biyo PREMIUM TIMES HAUSA domin ku ji yadda abin ya faro da kuma yadda a ƙarshe bayan Kiristoci sun ƙwace Spain da Portugal, su ka bai wa miliyoyin musulmi zabi uku: Ko ka fice daga ƙasar, ko ka koma Kirista, ko kuma a fille kan ka…

Shekarar 711: Farkon Jihadi A Cikin Kasar Spain:

Cikin wannan shekara ce, wato a zamanin Daular Umayyawa, dakarun mayaƙa daga na ƙabilun ‘Berber’ ko Maurus, ko Moors, na Afrika ta Arewa a ƙarƙashin wani Janar mai suna Tariq bin Ziyad, su ka fara kutsawa cikin ƙasar Hispania, wadda a lokacin Larabawa ke kira Andalus (Andalusiya), wato yankin da a yanzu ya kasance Spain da kuma Portugal.

Turawa masana tarihi ba su yarda cewa tun zamanin mulkin Sayyadina Usman (RA) ‘yan jihadi su ka shiga Andalus ba, kamar yadda masanin tarihin Musulunci Aɗɗabari ya da kuma Ibn Kathir su ka rubuta ba.

Amma dai bangarorin biyu duk sun haƙƙaƙe cewa ƙasar Andalus ta kasance a ƙarƙashin Daular Musulunci, har sai cikin shekarar 1491 da aka kammala ƙwace garuruwan Sarakunan Musulunci, duk su ka koma a ƙarƙashin ikon Sarakunan Kiristoci.

Abin da Turawa masana tarihi su ka fi amincewa da shi, Andalus kusan kashi biyu bisa uku na ƙasar (2/3) ya shafe shekaru 375 a ƙarƙashin Daular Musulunci. Daga nan kuma rabin ƙasar ya kasance a hannun Daular Musulunci, bayan Kiristoci sun fara ƙwace wasu yankuna. A ƙarshe kuma bayan ƙwace sauran garuruwa, Masarautar Granada ce kaɗai ta rage tsawon shekaru 244 a ƙarƙashin Musulunci, wadda ita ma cikin 1491 aka cinye ta da yaƙi.

Lokacin da mayaƙan jihadi su ka fara shiga Andalus cikin 711, sun fara murƙushe dakarun Visigoth a ƙarƙashin Sarkin su Roderic a Yaƙin Guadalete, cikin 712. Kuma sojojin sa ba su wuce 1,700. Wannan nasara ta sa an ƙaro masu dundunonin mayaƙa akasarin su Larabawa a ƙarƙashin Janar Wali Musa Ibn Nusayr, kuma ya na sama da Tariq Ibn Ziyad.

Mayaƙan da ke ƙarƙashin Musa Ibn Ziyad sun kai 18,000. Sun murƙushe Seville da Merida, inda su ka haɗe da dakarun da ke ƙarƙashin Tariq a Telavera.

Cikin shekarar 713 mayaƙan jihadi su ka mamaye Galicia, Leon da Zaragoza.

Bayan sauran garuruwa irin su Cordova duk sun koma ƙarƙashin Daular Musulunci, mulkin Banu Umayya ya zo ƙarshe Shaam/Siriya/Damashƙa bayan Abbasiyawa sun ƙwace mulki, hedikwatar Musulun ci ta tashi daga Dimashƙa ta koma Bagadaza, a cikin 750.

Cikin shekarar 756, sai ɗaya daga cikin Sarakunan Banu Umayya da ya tsira ba a kashe shi ba, mai suna Abdul-Rahman, ya danno cikin ƙasar Andalus, ya ƙwace mulki a Daular Musulunci ta birnin Cordova, kuma ya k
ƙwace Seville, ya ayyana kan sa a matsayin ‘Amirul Mumina’ na Musulmin duniya, ya ce ba zai yi mubayi’a ga Amirul Muminin na Daular Abbasiyawa a Bagadaza ba.

Sarki Abdul-Rahman ya ƙwace Cordova, kuma birnin ya ci gaba da zama birnin Daular Musulunci na Andalus, har tsawon ɗaruruwan shekaru.

Tsawon shekaru da dama Musulunci na ƙara mamaye Spain, har dai cikin shekarar 914, aka ci birnin Barcelona da yaƙi.

Dakarun Almorabid sun ƙwace birnin Lisbon (hedikwatar Portugal a yanzu), a cikin shekarar 1086. Ganin yadda aka mamaye kusan fiye da rabin ƙasar, musulunci ya shimfiɗu a Andalus, sai Sarakunan Kiristocin da su ka rage ba a mamaye ba, su ka yunƙura domin ƙwato ƙasar su.

‘RECONQUESTA’: Yaƙuƙuwan Korar Musulmi Daga Andalus (Spain da Portugal):

An fara wannan gagarimin shiri daga shekarar 1097. Cikin shekarar 1118 dakarun Kiristoci su ka ƙwace biranen Tuledo da Zaragoza. Cikin 1147 an ƙwace birnin Lisbon daga mulkin mayaƙan Almorabid.

A shekarar 1248 an ƙwace birnin Seville, sai Cardiz da Cordoba kuma aka ƙwace su a shekarar 1236.

Daidai shekarar 1249, duk wani Sarkin Musulunci a ƙasar Spain an ƙwace sarautar sa, ta koma hannun sarakunan Kiristoci. Sai birnin Granada kaɗai ya rage, wanda aka yi ta gwabzawa, ba a samu yin galaba an ƙwace shi ba, sai cikin shekarar 1491 ya faɗa hannun Kiristoci.

Me Ya Riƙa Biyo Baya?

Daular Andusiya ta Musulunci ta yi shahara sosai wajen ci gaba iri-iri daban-daban. An riƙa gina manyan masallatai da danƙara-danƙaran gidaje da fadar alfarma ta sarakuna.

Amma da sarakunan Kiristoci su ka hau mulki, an riƙa rusa wasu, wasu masallatan kuma aka riƙa maida su coci-coci. Fadar sarakuna da manyan gine-gine an riƙa maida su dandalin hutawa, sheƙe-aya da masha’a.

Tun kafin Granada ta yi saranda, duk garuruwan da Sarakunan Kiristoci da mayaƙan su su ka ƙwace, da farko an riƙa barin musulmai su riƙa yin addinin su. Amma daga baya sai aka riƙa kafa dokoki. Kowane Sarki ya riƙa kafa ta sa dokar, musamman manyan Sarakuna uku na ƙasar tare da manyan limaman Kiristocin ƙasar.

An riƙa kafa sharuɗda uku: Mai son ci gaba da zama Andalus ya fita daga addinin Musulunci. Haka duk wani Bayahude shi ma ko dai ya koma Kirista ko ya fita. Sharaɗi na uku kuma, wanda bai zabi ɗayan-biyun ba, to za a kashe shi.

A daidai shekarar 1942, masana tarihi sun ƙiyasta cewa musulmin da su ka rage a Andalus ba su wuce 500,000 a lokacin.

Cikin 1499 Achbishop nFrasisco da Cardinal Frasisco Jimenez na Granada sun ƙara matsa-ƙaimi wajen tilasta wa musulmai su shiga addinin Kirista dolen-dole.

An wayi gari a cikin 1501 babu sauran musulmi ko ɗaya a Granada, daular da ta shafe shekaru ɗaruruwa matsayin daular musulunci mai ɗimbin tarihi.

Ganin haka, sai Sarauniya Isabella ta Castellia ita ma ta shimfiɗa dokar tilas kowa ya koma Kirista kawai, a cikin 1502.

Shi ma babban Sarkin Aragon, a cikjn 1515 zuwa 1520, ya maida kowa Kirista.

A cikin 1524, manyan Sarakunan Andalus su ka nemi Paparoma Clement VII ya amince a haramta addinin musulunci a Andalus/Spain/Portugal. Kuma haka aka yi. An kafa wannan dokar a cikin 1525

Sai dai kuma sarakunan musulunci da sauran waɗanda ba su iya jure wulaƙanci, sun riƙa yi hijira su na komawa Afrika ta Arewa.

Amma kuma wasu da su ka koma Kirisroci a sarari, sun riƙa yin addinin su na musulunci a asirce.mahukunta sun riƙa yin zargin haka. Aka riƙa azabtar da wasu da dama. Ta kai cikin 1614 an kakkabe duk wani mai launin fatar da ake zargin sa, sun fice daga ƙasar.

Share.

game da Author