Duk mai fatan Najeriya ta dagule, bai ɗanɗani wahalar Yaƙin Basasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

0

Sanata Abdullahi Adamu, kuma tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, ya bayyana cewa masu tada-ƙayar-baya da kartar ƙasa wai sai an raba Najeriya, duk hayaniyar banza ce su ke yi, sun san Najeriya ba za ta taba rabuwa zuwa shiyyoyi a matsayin kowace ƙasa mai zaman kan ta ba.

Da ya ke magana a lokacin da Jakadan Tanzaniya a Najeriya, Benson Bana ya kai masa ziyara a Abuja.

Adamu ya bayyana cewa ya na da yaƙinin cewa Najeriya ba za ta taba rabuwa ba, sai dai a yi ta surutai marasa amfani da hayaniya kawai.

“Taya Najeriya za ta rabu? Su masu hauragiyar sai a raba Najeriya, dukiyoyin mafi yawa su na Arewacin ƙasar nan, kuma a Arewa ɗin su ke harkokin na su.

“Sannan ina ƙara tabbatar maka cewa masu wannan hayaniyar yawan da ‘yan ƙabilar su a Arewa, sun fi na yawan al’ummar su da ke zaune can kudu ɗin a jihohin su.”

Adamu ya shaida wa jakadan cewa dole za ta kasance akwai sabani tsakanin bangarori ko ƙabilu. Amma kamata ya yi a riƙa amfani da sabanin ana ƙarfafa zamantakewa da juna, ba wai ƙoƙarin haddasa fitina ko husuma ba.

Yayin da ya ke gargaɗi da bayar da shawara cewa masu tayar da jijiyoyin wuya su daina, Adamu ya tunatar da su abin da ya ce ba su sani ba.

“Ire-iren mu da mu ka san lokacin da aka yi Yaƙin Basa, ba za mu taba addu’ar sake maimaita irin wancan balbalin bala’i ba.

“Ba na fatan tserewa na bar Najeriya, saboda ba ni da wurin guduwa ko na tsere. Ba na mafarki ko fatan zama wata ƙasa in banda Najeriya.”

Adamu ya yi wannan kalami ne daidai lokacin da kisan-gillar da aka yi wa Ali Gulak a Jihar Imo ke ci gaba da janyo ka-ce-na-ce a ƙasar nan.

A Kano an nemi a tayar da ƙura bayan an ƙona motocin ɗaukar kayan man ja guda biyu, da jarkoki kusan 1,000 na manja mallakar ‘yan kasuwar Kano a Kudu maso Gabacin ƙasar nan.

A yankin na jihohin ƙabilun Igbo dai an riƙa banka wa ofisoshin ‘yan sanda wuta, kuma ana bin su ana kashewa. Sannan kuma an banka wa ofisoshin Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) masu yawa wuta.

Share.

game da Author