Direbobi ke haddasa haɗurran da ake asarar rayuka masu yawa a manyan titinan ƙasar nan -Gwamnatin Tarayya

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa yawan mutanen da ke mutuwa a haɗurran motoci kan manyan titinan ƙasar nan, sun haura yawan waɗanda cutar korona da cutar zazzaɓin maleriya ke kashewa a kowane wata.

Ministan Ayyuka Raji Fashola ne ya bayyana haka, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa.

Fashola ya bayyana cewa a rahotannin da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ke bai wa Gwamnatin Tarayya a kowane ƙarshen wata, an tabbatar da cewa, “kashi 70 bisa 100 na haɗurran da ake yi duk direbobin mota ne ke haddasa su.

Sai dai Fashola bai ɗora laifin a kan rashin kyawon titina ba.

Ya ƙara da cewa manyan titinan da su ka fi cin rayukan jama’a a ƙasar nan, sun haɗa da titin Lagos zuwa Ibadan, titin Abuja zuwa Keffi zarcewa Lafiya. Sai kuma titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Fashola ya ƙara da cewa, “kowane wata Hukumar FRSC na aika wa Fadar Shugaban Ƙasa adadin haɗurran da aka yi a kan manyan titinan ƙasar nan da kuma yawan mutanen da su ka mutu a sanadiyyar haɗurran. Ta Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ake aika wa Fadar Shugaban Ƙasa, ni ma su na turo min kwafe.

“Amma mun yi nazarin haɗurran Janairu 2020, Janairu 2019 da Janairu 2018, duk adadin waɗanda su ka mutu ya zarce adadin yawan mutanen da zazzaɓin maleriya da cutar korona ke kashewa

Ministan ya ce ana nan ana tsara hanyoyin rage yawan haɗurra a kan manyan titina.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta lura da yadda matafiya su ka fi ƙorafin cewa an fi yin haɗurraa wuraren da su ka lalace da kuma inda ake aiki kan titina.

Share.

game da Author