Dillalan gwanjon kayan sata su 2000 ke turereniyar neman kwangilar gwanjon kadarorin ɓarayin gwamnati

0

Akalla dillalan kayan gwanjon kadarori har su 2000 ne su ka nunawa gwamnati sha’awar karbar dillacin sayar mata da kadarorin da Gwamnatin Najeriya ta kwato daga hannun barayin gwamnati.

Shugaban Kwamitin Sayar da Kadarorin Satar Barayin Gwamnati, Belli Nasir ne ya bayyana haka a Abuja, a ranar Alhamis a lokacin taro da dillalan.

“Mun karbi takardun neman dillancin kadarorin daga mutane daban-daban da kuma kamfanoni daban-daban za su kai 2000.”

Akalla za a sayar da kadarori daban-daban a wurare har 25.

Kafin dai a bude shirin neman dillancin, Shugaban Kwamiti kuma Babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a, Dayo Apata ya ce kwamitin ya tantace wurare 25 da za a je a sayar da kadarorin barayin gwamnati a fadin kasar nan, baya ga wadansu kadarorin da ke yankunan da ake fama da matsalar tsaro.

“Masana darajar gine-gine da filaye duk sun bi sun tantance adadin darajar kowace kadara, domin a tabbatar da an sayar a farashin kasuwa.”

Apata wanda shi ne Babban Lauyan Gwamnatin Najeriya, ya ce ba za a kauce ko a karkace daga bin ka’idojin da kwamitin sa mai mambobi 14 ya gindaya wajen zaben dillalan ba.

Ya kara da cewa duk wadanda su ka shiga aikin yanka wa kadarorin farashi, to ba za su shiga ciniki a ranar da za a kada wa kadarorin kararrawa ba.

Sannan su ma mambobin kwamitin an haramta masu shiga.

Share.

game da Author